Hadin- gwiwar Duniya: Ana bukutar biliyoyin dala domin yakar Korona.

Mista Tedros Andhanom Dhebreyesus

Tura wannan Sakon

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ruwaito cewa, akwai matukar bukatar rarraba alluran riga-kafin kamuwa da annobar Korona a kasashe masu tasowa. Wata sabuwar dabarar da hukumar lafiya ta duniya(WHO) ta tsara,na bukatar zunzurutun dalar Amirka biliyan 23 da digo 4 domin tabbatar da daidaito wajen wajen rarraba alluran na riga-kafi zuwa sassan duniya,a karo na farko cikin watanni uku.

Samar da kudaden,za ta taimaka matuka gaya wajen ceto rayuka fiye da miliyon 5 da digo 3. Shugaban hukumar lafiya ta duniya( WHU) Mista TedrosAndhanom Dhebreyesus,ya ce, tuñi hukumar ta samar da alluran riga-kafi miliyan 425 ga kasashe 144.

Ya ce, kusan gwaje-gwaje miliyan 130 aka gudanar tare da samar da iskar gas da na’urar kare-kai da hanyoyin magance cutar kusan a ko’ina a duniya. Sai dai matsalar kudi ta hana tsare-tsaren rawar gaban-hantsi,inda ya kara yin kira da a yi hattara a wani taron ‘ yan- jarida da ya kira a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya.

Daga nan ya yi gargadin cewa, matsawar ba a dauki matakan shawo kan cutar ba, za ta ci gaba da yaduwa a ko’ina cikin duniya. Yaduwar annobar ta zama tamkar wutar- daji aTurai da sauran sassan duniya kuma cikin watanni biyu kacal ta fi yin kamari babu kakkautawa.

Daga nan ya yi roko ga kasashen nan 20 (G20)masu karfin tattalin arziki da su kawo dauki gaggawa kafin abin ya gagari Kundila

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *