Haduwar tsofaffin dalibai ta jaddada zumunci -Lawan Mahmud Bello

Lawan Mahmud Bello

Tura wannan Sakon

Daga Alhussain Kano

An bayyana cewa, Babban makasudin gudanar na taron tsofaffin dalibai ana yi ne domin hada zumunci a hadu da wanda aka jima ba’a gani ba a tattauna al’amura na rayuwa da tuna kuruciya ta haduwar makaranta.

Babban Sakatare a hukumar klbashi da Fansho na jihar Jigawa, Alhaji Lawan ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a yayin taron shekara na kungiyar tsofaffin dalibai na Garki da aka gudanar a harabar makarantar.

Ya ce, suna yara suka shiga makarantar shi ya shiga a 1977 zuwa 1982 kuma daga wancan lokaci zuwa yanzu, sun ga canje-canje da suka gama makaranta, wadansu sun shiga jami’a sun gama sun kama aikin gwamnati, wanda yanzu ya kai ga matsayin da yake kai na babban Sakatare a jihar Jigawa.

Ya nuna jin dadin haduwar su ta zumunci da suka yi, sun zauna sun tattauna rayuwa da dimbin mutane da suka zo mazansu da mata duk da halin tsananin rayuwa da ake ciki.

Wadansu sun zo da ya’yansu da matansu domin bunkasa zumunci. Babban Sakataren na hukumar albashi da fansho, Alhaji Lawan Mahmud ya ce, ilimi yanzu ba kamar yanda aka ba su shi a baya ba ne, domin ita kanta makarantar asalinta ta horon malamai ce, amma abin takaici yanzu ma an rushe tsarin na makarantun horon malamai, wanda hakan ya kwari Arewa domin haka ya kamata a farfado da makarantar horon malamai.

Ya ce, karatu da aka koyar da su a baya da tarbiyya yake tafiya, Malamai da suka koya masu ilimi har akwai ‘yan kasashen waje ‘yan Filifin da Indiyawa kuma ba Musulmi ba ne, amma sun koya masu tarbiyya ta kyautata rayuwarsu, sun dora su kan hanya da suka taso ake sha’awarsu saboda dabi’u masu kyau wanda yanzu an rasa su.

Ya yi nuni da cewa, al’umma na da rawar takawa wajen kyautata tarbiyyar ya’ya domin gwamnati ba za ta iya komai ita kadai ba, sai mutane sun taimaka sun agazawa kansu, saboda tabarbarewar tarbiyya domin ita tarbiyya takan fara daga gida ne, idan aka sami kyakkyawan tushe, idann Allah ya yarda komai zai zo cikin sauki.

Yanzu akwai wadata amma matsalar babu kwanciyar hankali wanda a baya kuwa babu wadata sosai, amma suna iya yin abin da mutanen yanzu basa iyawa musamman na sadar da zumunci da taimakekeniya, kuma su zauna lafiya, shi yasa shugabannin baya suka fi jin dadin gudanar da abubuwansu.

Babban sakataren Alhaji Lawan Mahmud Bello ya ce, makarantar Garki ta yaye dalibai da suka yi fice a bangarori da dama ayyuka kama daga jami’an tsaro da ma’aikatan gwamnati da sauran fannoni kuma suna taimaka wa ci gaban makarantar gine-gine da sayen magunguna da samar da ruwan sha wanda shi kansa a lokacin da yake ma’aikatar ruwa ta Jigawa ya sa ana samar da mai lita 200 a kowane wata domin amfanin makarantar, sannan ana haduwa ana tallafa wa masu karamin karfi a tsakaninsu.

Shi ma Alhaji Mustapha Bako Babura daya daga tsoffin daliban dan aji na 1984 wanda ma’aika ci ne a sashen kula da lafiya a matakin farko na karamar hukumar Babura ya ce, taron na da muhimmanci da wanda a irin sa ne za a san irin halin da wani yake ciki aga irin taimako da za’a yi masa, sannan za a sada zumunci wanda Musulunci ya yi umurni da hakan. Taron na tuna masu irin zaman makaranta da aka yi shekaru fiye da 30.

Mustapha Bako ya yi nuni da cewa, ba zaa hada ingancin ilimi na baya dana yanzu ba, domin haka akwai bukatar gwamnati da sauran al’umma a hada hannu domin bunkasa ci gaban ilimi, ya kuma yaba da irin kokari da gwamnatin jihar Jigawa take yi wajen bunkasa ci gaban ilimi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *