Hafsat Ganduje ta nusar kan muhummacin awon ciki

A gangamin siyasa: Alpha Dambatta ta jinjina wa Farfesa Hafsat Ganduje

Tura wannan Sakon

Daga Usman Gwadabe

Uwar Gidan Gwamnan Jahar Kano, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje, ta kara tunatar da mata muhimmancin zuwa awon ciki da kuma kula da alluran riga-kafin da ake yi wa kananan yara.

Farfesa Hafsat Ganduje ta yi wannan tunatarwa ne a loka­cin da ta ke kaddamar da makon duba lafiyar mata masu dauke da juna biyu da kananan yara wanda gwamnatin Jahar Kano ta shirya karkashen Maaikatar Lafiya ta Jahar.

Mai Dakin Gwamnan ta kara da cewa sai da taimakon iyaye maza ne, mata za su samu damar baiwa yaransu kulawar da ta ka­mata kamar yadda addinin musu­lunci ya tanada.

Ta kuma kara da kiran maza da su rika tausayawa matansu masu Juna biyu ta hanyar kulawa da basu abinci mai gina jiki da kara lafiya.

Bayan nan ta raba kyaututtuka da kayan abinci masu gina jiki ga matan da suka zo asibitin domin yin awo da kawo yara rigakafi.

A nasa jawabin, Kwamishi­nan Lafiya, Dakta Aminu Ibra­him Tsanyawa, ya ce kasancewar cutar kyanda na saurin hallaka kananan yara ya sa Ma aikatar Lafiya ta Kasa ta mayar da yin rigakafi sau biyu ga kowane yaro a wata.

Dakta Tsanyawa ya kuma ce Ma aikatar Lafiya za ta ci gaba da yaki da cutar tarin fika da cutar yunwa da kuma cutar corona da dukkan cutar da ke saurin yadu­wa a tsakanin al’ummah.

A nasa bangaren, Mai Martaba Sarkin Rano, Alhaji Kabiru Mu­hammad Inuwa, ya yi karin haske ne bisa yadda ake karbar alluran a garin Rano tare da yin kira ga mata masu juna biyu da su mayar da hankali wajen cin abinci da zai kara lafiyar su da abunda su ke dauke da shi acikinsu da kuma su rika zuwa awon ciki, wannan na konshe cikin sanarwar da jami’ar yada labarai ta ma’aikatar lagfi­ya, Hadiza Mustapha Namadi ta bawa Albishir ranar Litinin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *