Hakuri, jajircewa sinadarin samun daukaka -Injiniya Sanusi Dahiru

Tura wannan Sakon

Daga Rabiu Sanusi Kano

An bayyana hakuri da jajircewa matsayin linzamai da ke kai kowane bawa ga samun nasara da daukaka a rayuwar mu. Shugaban kamfanin Precious Stone, Injiniya Dahiru Sanusi bayyana haka a wata zantawa da wakilinmu cikin makon da ya gabata a ofishinsa da ke cikin birnin Kano.

Injiniya ya ce, kamfanin ba shi ne kamfanin farko da ya fara zama ba, akwai kamfanin Strong Well da suka fara hada-hadar kasuwanci tare da abokinsa da yazama matsayin mai gidansa.

Sanusi ya ce, LOKACINyana yaro wajen Mai gidan sa, Malam Toufik ya samu dama matuka musamman yadda suka hadu tare da yin komai tare ba tare da jin zafin maigidan na sa ba har ta kai ta kawo sunan kamfanin na ogansa ne da nasa a hade domin gaskiya da rikon amana ba tare da mugunta ba.

Ya ce, daga bisani ne ya bukaci samun damar zama da kafarsa ne mai gidan nasa ya sahile mashi tare da taimakonsa ta fuskar da ya bukata daga gareshi ba tare da nuna jin zafi ba.

Shugaban kamfanin ya bayyana irin kalubalen da ya fuskanta yayin da yake san kafa kamfanin da a yanzu yake na daya daga cikin wadanda sukai fice a harkar gini da aikin hada ruwa da sauran kera kayan aiki wajen bunkasa noman zamani.

Wani abin alfahari a yau shi ne, yadda wani aiki da suka yi na noman rani na zamani ta hanyar hasken rana bayan sun kammala aikin a garin zariya suka tura ma abokan huddar su na kasar cin suka akwai gyara daya, amma precious sun tabbatar ma da wannan kamfani a sin cewa, yanayin gurin nada nasaba da gocewar wannan aiki dole sai an samu tsaiko daga bisa suka fahimci hakan daidai ne.

Idan aka juya bangaren aiki kuwa, Injiniya ya bayyana horas da yara da dama fanni daban-daban kama daga wadanda suke cikin gida da ma wadanda idan aiki ya zo ne ake kiran su domin aiki nan take a sallame su.

Ya ce, suna shirin fadada ayyukan su domin samun sanayya tare da aiki da sauran sassa na gwamnati, inda ya zuwa yanzu suna fatan samun kudin shiga da zai taimaka masu wajen kara bunkasa sana’arsu.

Injiniya ya bukaci gwamnati da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen taimaka ma matasa dan dogaro dakai,inda kuma ya garadi matasan da su rike gaskiya da rikon amana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *