Hana shigo da abinci Nijeriya, madalla da shugaban kasa -Muhammad Idris

Ayyukan raya kasa: Shugaba Buhari ya jinjna wa Ganduje

Shugaban Kasa Buhari

Tura wannan Sakon

Isa A. Adamu Daga Zariya

An bayyana matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka kan yadda ya bayar da umurnin kan iyakokin Nijeriya na za a shigo da kayyaki da dama amma ban da kayayyakin abinci musamman shinkafa.

Sakataren kungiyar manoman shinkafa a karamar hukumar Giwa Alhaji Muhammad Idris ya bayyana kalaman da suka gabata, a lokacin da wakilinmu ya zanta da shi, kan matakan da shugaban kasa ya dauka, na farfdo da noma a tarayyar Nijeriya , musamman nomad a shugaban ya dauka na tabbatar da ci gaba das a ido ga bangaren noma na ganin ba a koma gidan jiya ba.

Alhaji Muhammad ya ci gaba da cewar, babu ko shakka, hangen nesar da shugaban kasa ya yi na ci gaba da sa ido na ganin ba a ci gaba da bude kan iyakoki ba domin shigo da shinkafa ba,wannan cewarsa zai kara wa manoman shinkafa kwarin gwiwar ci gaba da noman da suke a sassan Nijeriya baki daya.

 Sakataren manoman shinkafa a karamar hukumar Giwa, ya kara da cewar, tun lokacin da shugaban kasa ya furta wannan kalma na gwamnatinsa za ta ci gaba da bin hanyoyin da duk suka dace, domin bunkasa a daukacin Nijeriya, ba jihohin da suke arewacin Nijeriya kawai ba.

Da kuma ya juya ga manoman shinkafa da aka ba su rancen noman shinkafa da har zuwa lokacin da aka zanta da shi, wasu da dama, in ji shi, sun yi kememe wajen cika alkawarin biyan ba shin da aka yi alkawari da su kafin a danka ma su kayayyakin da suka tallafa ma su wajen noman shinkafa da suke yi.

 Alhaji Muhammad ya kuma nuna matukar jin dadinsa da yadda shugabannin kungiyar manoman shinkafa ke gudanar da shugabancin da aka dora ma su, na yadda ako wane lokaci suke bakin kokarinsu na ganin manoman shinkafa a jihar Kaduna ba su fuskanci wata ko kuma wasu matsalolin da za su hana su ci gaba da noman shinkafa da suke yi, a nan sai ya yi kira ga daukacin manoman shinkafa da suke jihar Kaduna das u ci gaba da lura da alkawurran da suka yi, na cewar ko da ta Allah ta kasance a kan su ‘ya’yansu ko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *