Hanyar Kano zuwa Dayi zai bunkasa harkokin kasuwanci

Tura wannan Sakon

Daga Wakilinmu

Babu shakka mayar da hanyar Kano zuwa garin Dayi dake cikin karamar huku­mar Malumfashi a jihar Katsina, tagwayen hanya wanda Sanata Barau Jibirin daga jihar Kano ya samo daga gwamnatin tarayyar kasar nan abu ne mai kyau da duk wanda ya ke bin hanyar zai yi matukar farin ciki da murna da shi.

Bayanin ya fito ne daga bakin wani mai kishin al’umma da ya fito daga garin zangon Kabo da ke karamar hukumar Kabo a jihar Kano, Alhaji Mamuda Liman Zangon Kabo, a lo­kacin da yake nuna farin cikinsa a kan mayar da han­yar Kano zuwa garin Dayi .

Alhaji Mamuda Liman Zangon Kabo ya ce, ga duk mai bin hanyar yasan tana bukatar kulawar da ta dace daga gwamanatin ta­rayyar Nijeriya, saboda ta yi matukar lalacewa wanda hakan ke kawo yawaitar asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.

Idan an kammala han­yar zai kara bunkasa tatta­lin arzikin jihohin da suke amfani da hanyar kamar Katsina, Sokoto, Zamfara, da Kebbi, sannan kuma har ila yau manya da kananan garurruwar da ke hanyar za su samu saukin shigowa Kano a kan lokaci. Amma ya shawarci gwamnati da kuma wadanda za su gu­danar da aikin hanyar da su tabbatar sun mayar da han­kulansu, wajen kammala aikin cikin sauri ba tare da bata lokaci ba.

Sai ya nuna damuwar sa a kan yadda har zuwa yan­zu aikin hanyar Kano zuwa Abuja, ke tafiyar hawain­iya wanda haka ke jawo asarar rayuka da dukiyoyin al’umma. Sannan kuma dan kasuwar ya janyo hankulan gwamanti da ta himmatu wajen kawo karshen masu garkuwar da mutane da ake yawan yi da matafiya a manyan hanyoyin kasar nan wanda wannan na matukar kawo barazana ga harkokin sufuri a fadin Nijeriya.

Malam Mamuda Liman Zangon Kabo, ya koka ma­tuka game da yadda gwam­natin kasar nan ta yi karin kudin kudin Fetur ba tare da ta sanar da al’umma ba , yawanci idan gwamnati ta yi karin yakan shafi talaka­wa da kuma tsadar kayan masarufi akasuwanni. Daga karshe, ya ce ka­rin kudin yafi shafar ta­lakawa kai tsaye, sai ya yi addu’ar Allah ya kawo mana karshen matsalo­lin tsaron da kasar nan ke fuskanta musamman na garkuwar da mutane

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *