Hanyoyin Nijeriya sun mutu murus –FERMA

Tura wannan Sakon

Hukumar kula da hanyoyin ta FERMA ta ce, akasarin hanyoyin Nijeriya da ake kallon su a matsayin tarkon mutuwa, duk sun zarta wa’adin ingancinsu kuma suna bukatar kulawar gaggawa. Shugaban hukunaar, Alhaji Nuruddeen Rafin-dadi, shi ya bayyana haka a yayin gabatar da wata makala a Kaduna.

Shugaban ya bukaci direbobi da su yi taka-tsantsan a yayin tukin motocinsu a kan manyan hanyoyi saboda yadda suka mutu murus.

‘Yan Nijeriya da dama ne ke rasa rayukansu sakamakon hadurran ababen hawa a kan hanyoyin da ke sassan kasar dabandaban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *