Harin ‘yan bangar siyasa: Lauyoyin Marafa sun tsallake rijiya da baya a kotu

A Zamfara: Marafa ya yi tir da kai wa ‘ya’yan PDP hari

Senator Marafa

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

An bayyana cewa, lauyoyi masu kare Sanata Kabiru Garba Marafa sun tsallake rijiya da baya, sakamakon harin ‘yan bangar siyasa bayan kammala zaman kotun a Gusau.

Hakan ya fito ne daga bakin jami’in yada labarai na jam’iyar APC, bangaren Sanata Kabiru Garba Marafa da Bello Bakyasuwa a lokacin da yake yi wa manema labarai bayani a Gusau da yammacin jiya. Bello ya kara da cewa, kamar yadda aka saki suna da zaman kotun a jiya wanda Sanata Kabiru Marafa ya shigar yana kalubalantar jam’iyyar APC ta kasa kan laifuffuka dabandaban.

Ya ce, bayan zaman kotun ne sai aka gayyato wadansu ‘yan bangar siyasa, suka yi kokarin dukansa, a kokarinsa na shiga motar lauyansu ne wadansu suka yi masa mari biyu, wanda ganin hakan suka kama motar lauyoyin na su da duka ya fita a tsiyace.

Bello ya kara da cewa, haka suna ji suna gani suka bar lauyansu guda daya, wanda sai da ya yi garkuwa da kwamishinan Shari’a na jihar Zamfara.

Ya kara da cewa, al’amarin bai ba su mamaki ba, saboda tun kafin lokacin wadansu sun kira shi suka gargade shi kan cewa, ka da ya kuskura ya halarci zaman kotun na jiya, sai dai yaga be da ce a ce yaki zuwa kotun ba.

Bakyasuwa ya ce, wani abin da ya fi ba su mamaki shi ne yadda za’a ce a cikin harabar kotu a yi ta’addancin wanda a gaban kowa kamar jami’an tsaro da ‘yan jarida, ya ce, idan in har aka ce ba ka da aminci a gidanka ba ka da shi a kotu to babu inda za ka same shi.

Ya ce, muna kira da babban murya ga jami’an tsaro da su zakulo duk wadanda suke da hannu cikin abin da ya faru, kuma su dauki matakin na gaggawa”in ji Ya kara da cewa, idan jami’an tsaro suka ki daukar mataki, nan gaba za su dauki mataki na kare kai, ma’ana za su kare kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *