Hasashen Dan-Pass: Siyasar gida-gida ta sami gindin zama a Kano

Alhaji Gambo Dan-pass
Daga Aliyu Umar( editan Albishir)
Dan-siyasa kuma hamshakin dan- kasuwa,Alhaji Gambo Dan-Pass ya bayyana fargabar wargajewar akidar siyasa a Kano matsawar ba a kawar da siyasar gida-gida ba.
Dan-Pass ya jima da godon ganin an manta da siyasar gida-gida a rungumi siyasar tabbatar da masalaha ga jama’a. Ya ce,ba daidai ba ne domin mutum ya yi gwamna ko minista ko kuma kowane irin shugabaci,ya yi watsi da take jam’iyyar da ta yi silsar hawansa kan mukamin.
Dan-Pass wanda aka fi saninsa da kasancewar na hannun dama Alhaji Muhmmadu Abubakar Rimi, gwamnan Kano daga 1979-1982, ya yi ikirarin cewa, muddin siyasar gida-gida ta sami gindin zama a Kano, to, sai fa ‘yan-siyasa su fara shirin daukar alhakin tabarbarewar jagorancin jama’a,kada su zargi kowa ko a rediyo ko a kotu da laifin tabarbarewar.
Ya ce, akidar Rimi ita ce, kare talaka daga danniya da tursasawar azzaluman shugabanni.
A saboda haka,ya jaddada matsayinsa kan kyamatar siyasar gida-gida amma ba rike uban-gida ba kamar yadda ya rike Rimi.
A karshe,ya yi fatan ‘yan-siyasa za su hada kai domin ceto talaka daidai da kudurin mutanen Kano na ceto al’umma daga kangim tursasawa na wadanxsu jagororin jama’a.