Hauhawar farashin kayan masarufi, da walakin -Nasiru Mato

hauhawan kayan masarufi

Hauhawar kayan masarufi

Tura wannan Sakon

Labarai Yusuf M. Tata Damaturu

An bayyana cewa hauhawar farashin kayan masarufi da ake fama da shi a kasuwa ba laifin ’yan kasuwa ba ne, a cewar shugaban gamayyar kungiyoyin ’yan kasuwa na karamar hukumar Potiskum da ke jihar Yobe, Alhaji Nasiru Mato a lokacin da yake zantawa da Albishir, a ofishinsa da ke Potiskum.

Alhaji Nasiru Mato, wanda shi ne, shugaban kamfanin MATO MULTI LINK ya ce, karin kudin man dizel da fetur a kasar nan shi ne makasudin tashin goron-zabi da aka samu a kasuwanni da shagunan sayar da kayayyakin amfanin yau da kullum.

A cewarsa, kafin a sami karin kudin man dizel da na fetur, manyan motocin daukar kaya sukan dauko kayan masarufi daga Ikko zuwa arewacin kasar nan, a kan kudin da bai wuce Naira dubu dari shida (N600,000.00) ko ma kasa da haka ba, amma a yanzu ana biyan tsabar kudi sama da Naira miliyon daya (N1,000,000.00) wajen dauko kayan daga Ikko zuwa arewacin Nijeriya.

Alhaji Nasiru Mato ya ce, akwai bukatar gwamnatin kasar nan ta dunga tallafa wa kananan ’yan kasuwa da manoma da kuma makiyaya.

A cewarsa, tattalin arzikin kasar nan yana samuwa daga wadannan mutane baya ga man fetur da wadansu ababe da gwamnatin tarayya da sauran jihohi suke sarrafawa. Ya kara da cewa, gwamnatin tarayya, musamman shugaban kasa ya kamata ya dinga sara yana duban bakin gatari wajen yanke hukuncin karin farashin man fetur ko na dizel, saboda sakamakon karin yakan dawo kan talakan Nijeriya ne, saboda babu dan kasuwar da zai biya kudi mai tarin yawa wajen dauko kayan kasuwancinsa, sannan ya rage farashin kayan da ya sayo ba tare da la’akari da ribar da zai samu ba.

Talakawan kasar nan a cewar shugaba Nasiru Mato, su dukufa da addu’ar neman saukin rayuwa da fatan Allah ya kawo alkairi a kasa, ya sanya albarka a cikin harkokin yau da kullum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *