Hausawa sun mamaye sana’ar sayar da kifi -Sani Lawal

Sani Lawal
Sana’ar kifi mai kankara sana’a ce da mafi akasarin masu yin ta ba Hausawa ba ne, amma ya zuwa yanzu Hausawa sun yi mata kaka-gida. Wakilinmu RABI’U SANUSI KATSINA ya sami zantawa da shugaban kungiyar masu sayar da kifi mai kankara na jahar Kano, ga kuma yadda hirar ta kasance.
ALBISHIR: Da farko masu karatu za su so jin da wa muke tare? Ni dai sunana Alhaji Sani Lawal Sani, kuma ni ne shugaban masu sana’ar sayar da kifin kankara da ke nan bayan dogon Banki da ke kan titin zuwa Zariya, a nan jahar Kano.
ALBISHIR: Ko za ka bayyana mana ya sana’ar kifi mai kankara take? Kusan ita wannan sana’a ta kifi mai kankara sana’a ce wadda za mu iya cewa a lokutan baya ba kasar Hausa take ba, asali Yarabawa ne suka zo mana da ita, amma yanzu ga shi yaran gida su ne suka juya ya zuwa iyayen gida, dalili kuwa shi ne, lokacin da muka fara ta, Yarabawa ne suke kawo kifin daga kasashen ketare kuma mu yi musu aikin samun dogaro da kai, amma a halin yanzu kusan mu ne muke jan ragamar kasuwancin gaba daya. Haka kuma kusan da an fi sanin kalar kifi kamar su sukumbiya da tarwada, amma zuwan kifi mai kankara wanda a halin yanzu yakara sa kasuwar tana kara bunkasa, sannan kasan kuma akwai kalar kifi yafi dari, kama daga kuroka da sukumbiya da fako da sabalo da sardine da shawa da tuna da dai sauransu.
ALBISHIR: Kasancewar wannan kifi ba a kasar nan ake samar da shi ba, ko zaka fada mana hanyoyin da kuke bi dan shigo da shi Nijeriya? Kusan kamar yadda kace ba a nan kasar ake samar da shi ba, haka ne wannan, shigo da kifi kamar shigo da mai ne ko fitar da shi zuwa wata kasa, dan haka ne wasu lokutan za ka ji gwamnati ta ce ta kashe makudan kudade wajen shigo da shi. Haka shi ma kifi lasisi ake bayarwa kamar sauran kayan da ake shugowa da su ta ruwa daga jihohin da su ke da ruwa kamar daga Fatakwal ko Warri ko Legas, daga nan ne mutanenmu za su je wadannan jahohi dan su sayo ya zuwa jahohinmu na nan.
ALBISHIR: Ko kuna kiwon irin wadannan kifayen a nan? Gaskiya a nan ba ma noman irin wadannan kifayen masu kankara, saboda ba zai iya rayuwa a nan ba. Kusan irin wadanda muke nomawa a nan su ne, karfasa ko tarwada, kuma ita ma ba ko ina ba ta fi yawa a kudancin kasarmu, amma kuma zan iya cewa akwai ruwan da idan ka jefa wani kifin ba zai iya rayuwa ba.
ALBISHIR: Kusan za mu iya cewa ya zuwa yanzu gwamnati ba ta da damar daukar duk matasan da su kai karatu aiki, daga bangaren ku wane hobbasa kuka yi ga matasa? Da ma kasuwar ta matasa ce kai tsaye, saboda haka idan ka zagaya kusan wannan kasuwar ta mu ce. Za ka ga duk yawanci matasa ne manyan kalilan ne, duk da cewa mun yi karatu bakin gwargwado amma mun fi mayar da hankali ga wannan sana’a. Kusan muna daukar matasan mu dauki kifi mu ba su domin su shiga cikin gari su sayar su sami abin da za su dogara da kan su, in da da safiya ka zo nan to kafin ka shigo nan ma sai ka yi da gaske kasancewar yawan matasan da ke daukar kifin, kuma kusan da wannan mu ke rage wa gwamnati matasan da ba su da aikin yi, kasan rashin aiki ko sana’a ga matashi ba karamar illa ba ne, ko ka same shi yana shaye-shaye ko dauke-dauke ko wani abin da zai kawo rashin kwanciyar hankali ga al’ummarmu. Idan aka samar masa da abin yi ne zai dauke masa hankali daga barin aikata mummunan aiki. Idan ya dauki tallan kifin har yakan manta da wasu abokai ko makamantansu.
ALBISHIR: yaya dangantakar kungiyarku da gwamnati? Za mu iya cewa danjuma ne da danjummai, dan kuwa mu dama karkashin ma’aikatar kula da kasuwanci muke, kowa ya san wannan, dan kuwa akwai kyakkyawar fahimta da gwamnati da ta ke ba mu damar fadin dukkan bukatinmu tare da ba mu shawarwari da fada mana idan gyara ya taso domin mu gyara. Idan ka duba a nan za ka ga kwamishinan muhalli har lambar yabo ya ba mu sakamakon mayar da hankali wajen tsabtace masana’antarmu, a maimakon a kama mu da laifi amma ka ga sai sambarka.
ALBISHIR: kusan mutum nawa ke gabatar da sana’ar? Ga wadanda su ke da rajista a wajenmu sun daram ma sama da mutum dubu goma a halin yanzu, kasan wasu daga nan idan sun dauka suna da yaran da suke ba su, su shiga gari ka ga su wadannan ba mu sa su a lissafi ba.
ALBISHIR: Wadanne nasarori ka samu a tsawon shekara uku da kake kan kujerar shugabanci? Zan iya cewa babbar nasara ita ce ta yadda muka ja matasa a jiki tare da samar masu sana’ar dogaro da kai. Sai batun tsabtace masana’antarmu da a baya idan mutane za su wuce ta nan sai sun toshe hancinsu, yanzu kuwa sai ma mutum ya wuce yana leken mai ake yi a nan. Haka kuma akwai batun zamantakewa ta kirki da zaman lafiya tare da aiki kafada da kafada da gwamnati. Sannan a tsaye muke don ganin an magance matsalolin da za su iya tasowa a ko da yaushe da dai sauran su.
ALBISHIR: Mece ce bukatarku a wajen gwamnati? kusan ko yaushe bukatar mu ga gwamnati bata wuce rokon samar mana da guri na din-din-din da mu ma za mu samar da dukkan abin da muke bukata domin idan ka dubi wannan guri sai dai a dan zauna kawai ba dan ya wadatar da mu ba.
ALBISHIR: matsalolinku fa? A lokutan baya mun sha fama da matsalar wutar lantarki, amma zuwana wannan kujera mun yi duk mai yiwuwa kuma mun yi nasara tsakanin mu da kamfanin wutar lantarki, ya zuwa yanzu ta zama tarihi. Sai matsala ta biyu batun gurin sana’a na din-din-din da muke fatan gwamnati na bakin kokarinta domin samar mana.
ALBISHIR: Ko kana da abin da za ka kara fada? Gaskiya akwai godiya ga kwamishinan muhalli bisa yadda suke sauraron mu tare da ba mu shawarwari kan abin da shige mana duhu, haka zalika godiya ta musamman ga Khadimul Islam Dokta Abdullahi Umar Ganduje bisa yadda yake kula da mu, sannan muna mika godiyarmu ga abokan sana’a tare da ba su hakuri wajen kara samar da ci gaba mai dorewa domin bunkasar kasuwancinmu.
ALBISHIR: Mun gode. Mu ma muna godiya.