Hawan bariki a Zariya: el-Rufa’i ya yi tsokaci kan tsaro

Hawan bariki a Zariya: el-Rufa’i ya yi tsokaci kan tsaro

Gwamna el-Rufa’i

Tura wannan Sakon

Isa A. Adamu Daga Zariya

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’I yay i kira ga al’ummar Nijeriya da a tashi tsaye na yin addu’o’I, domin kawo karshen matsalolin tsaro da ke addabar Nijeriya musamman wasu jihohi a arewa, ta addu’o’I ne kawai, a cewarsa, matsalolin tsaro za su zama tarihi

. Gwamna Nasir ya bayyana haka ne a lokacin da ya gabatar da jawabinsa ga al’ummar masarautar Zazzau, a ranar talatar da ta gabata, wajen Hawan Bariki da mai martaba Sarkin Zazzau yay i shi da wasu daga cikin Hakimansa da ya gudana a Unguwar turawa da ke [ GRA] ] a Zariya.

Ya ci gaba da cewar, gwamnatin tarayya ta ce ta nab akin kokarin ta na kawo karshen matsalolin tsaro, kamar yadda gwamnatin jihar Kaduna key i, amma duk da haka, a cewarsa, a kullun tunaninsa yay a za a kawo karshen wannan matsala ta tsaro a jihar Kaduna ya fahimta cewar, addu’o’I su ne mafita.

A nan ne yay i kira ga mai martaba Sarkin Zazzau da ya ci gaba da kokarin da yak e yi, na addu’o’in da za su kawo karshen matsalolin tsaro, musamman a jihar Kaduna da kuma Nijeriya aki daya, hakan ne kawai mafita, in mai martaba ya kara azzama, kamar yadda gwamnan jihar Kaduna Malam ya bayyana.

Da kuma ya uya ga zaben shekara ta 2023, gwamna ElRufa’I yay i kira ga al’ummar jihar Kaduna da su zabi mutane nagari da za su kamala ayyukan da gwamnatinsa ta fara a sassan jihar baki daya, a cewarsa, zaben mutane da suke kishin jihar Kaduna da kuma al’ummar jihar, a cewrsa, shi ne babban abin da al’ummar jihar za su duba kafin zaben shekara ta 2023.

Ya kara da cewar, ya ce za su tsayar da mutane nagari da suke da kishin jihar Kaduna da kuma al’ummar jihar a zaben 2023, abin da ya rage kamar yadda ya ce, sai al’ummar Kaduna su zabi mutane da babu abin da ke zukatansu, sai makomar jihar Kaduna, ba makowarsu, bayan sun bar kujerun da aka zabe su a kai ba.

Da kuma yak e tsokaci kan matakan da za su kawo karshen matsalolin tsaro a jihar Kaduna, gwamna El-Rufa’I ya nuna jin dadinsa tare da goyon bayan mai martaba Sarkin Zazzau na matakan dawo da hanyoyin tabbatar da tsaro na dauri, inda duk wanda ya shiga gari, mai Unguwa lallai ne a sanar da shi, shi kuma ya sanar da nag aba da shi, har dai ya zuwa ga jami’an tsaro da babban aikinsu ne su tabbatar da tsaron lafiya da kuma dukiyoyin al’umma.

Tun farko a jawabinsa, Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya nuna matukar jin dadinsa na yadda gwamnan jihar Kaduna da kansa ya halarci Hawan Bariki a masarautar Zazzau, wannan a cewar mai martaba Sarki, wasu alamu ne da ke nuna gwamna El- Rufa’I na da tunanin al’ummar jihar Kaduna a zuciyarsa.

A jawabinsa yay aba wa gwamnan na ayyukan ci gaban al’umma da ya jagoranci aiwatarwa a sassan jihar Kaduna, musamman a masarautar Zazzau da kuma jihar Kaduna baki daya. Bayan kamala jawabai, bias al’adar Hawan Barki a masarautar Zazzau, Mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahed Nuhu Bamalli da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’I, sun ganawar da al’adar Hawan Bariki a Zazzau ta tanda, inda suka tattauna abubuwanda suka dace domin ci gaban al’ummar jihar Kadunamusamman masarautar Zazzau.

Kammala ganarwar mai Martaba sarki da gwamnan yay i, sai suka fiti, inda suka yi sallama da shi, Mai martaba Sarkin Zazzau da kuma sauran Hakimansa domin dawowa fadar Zazzau daga Unguwar turawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *