Hawan daba: Gwamnan Bauchi ya karbi bakuncin sarkin Bauchi

Gwamnan Bauchi ya karbi bakuncin sarkin Bauchi

Gwamnan Bauchi yayi karba sarkin Bauchi

Tura wannan Sakon

Jamilu Barau daga Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa ‘yan kasa ribar dimokuradiyya domin inganta rayuwarsu. Mohammed ya bayyana haka ne a yau a lokacin da ya karbi bakuncin Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Dokta Rilwanu Suleiman Adamu da ’yan majalisar masarautar Bauchi kan bikin Sallah iri-iri na bana a gidan gwamnati Bauchi

. A cewarsa, gwamna Bala Mohammed, sarakunan gargajiya na taka muhimmiyar rawa wajen karfafa tsaro da samar da zaman lafiya da hadin kan jihar Bauchi da Nijeriya baki dada. Ya kara da cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da mara wa baya tare da mutunta matsayinsu.

Ya danganta nasarorin da gwamnatinsa ta samu a bisa wwarin gwiwa da goyon baya da kuma gudunmawar da sarakunan gargajiya da al’ummar jihar Bauchi suke bayarwa inda ya kara da cewa, zai tabbatar da jihar ta sami matsayi mafi girma a dukkanin bangarori.

Bala Mohammed ya yi amfani da kafar sadarwar wajen yin kira ga ‘yan Nijeriya da su yi amfani da lokacin bukukuwan domin rarraba soyayya da inganta zaman lafiya da kuma taimaka wa marasa galihu da mutanen da ba su da wata fa’ida ta zamantakewa wanda a cewarsa zai zama alamar kishin kasa.

Gwamna Bala ya shaida wa taron cewa, duk wani isassun fadakarwa da tsare-tsare na tallafa wa manoma da kayan masarufi gwamnatinsa ta kammala domin haka akwai bukatar a mayar da martani ta hanyar amfani da abin da aka noma.

A nasa bangaren, Maimartaba sarkin Bauchi, Alhaji Dokta Rilwanu Suleiman Adamu ya yaba wa gwamna Bala bisa jin dadinsa da goyon bayansa ga sarakunan gargajiya baya ga daukarsu a kowane fanni na shugabanci.

Da yake yaba wa gwamnan bisa gagarumin nasarorin da ya samu a fannin gine-gine da gyaran manyan gidaje da kiwon lafiya da ilimi da tituna, sarkin ya wara da cewa, masarautar Bauchi za ta ci gaba da bai wa gwamnatinsa goyon baya.

Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin gwamna da Sanata Baba Tela da kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Y. Suleiman da sauran manyan baki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *