Hisbah ta jagoranci gyara makabartar Kuka Bulukiya

Hassan Falaki Kulkul A kwanan nan aka yi gangamin gyaran makabartar Kuka Bulukiya da ke karamar hukumar Dala, jihar Kano.
Taron ya sami halartar dimbin jama’a da kungiyoyin sa-kai da hukumar Hisbah ta Dala.
An shirya shi ne a sakamakon cushewar da makabartar ta yi da ciyayi da kuma gyara kaburburan da suka rufta sakamakon ruwan sama. Mahalarta sun yi kokari sosai wajen aikin kuma sun yi alwashin ci gaba da aikin domin tsabtace makabartar daga masu fakewa suna aikata munanan ayyuka.
Albishir ta tattauna da masu gudanar da aikin gayyar domin jin kalubalen da suke fuskanta, inda suka bayyana cewa, suna fuskantar rashin kayan aiki musamman kasa da yashi da burji da sauran kayan aiki sannan sun roki karamar hukumar Dala da gwamnatin jiha da su taimaka masu da kayan aiki da kuma gyara fitilun makabartar da sauran makabartu da ke jihar.
Daga karshe, sun yi kira ga sauran al’umma da su yi kokari domin ci gaba da gyara makabartun jihar mako-mako.