Hobbasa: Buni ya rarraba wa mata awaki Kimanin 1,780

Tura wannan Sakon

Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu

Gwamna Mai mala Buni na Jihar Yobe ya rarraba Awaki kimanin 1,780 ga mata 890 a kananan Huku­momi 17 da ke Jihar da aka gabatar a Garin Buni Yadi cikin karamar hukumar Gujba, don samar musu sana’a don dogaro da kai a matsayinsu na iyayen giji.

Da ya ke jawabi a yayin gudanar da bikin, Gwamna Mai Mala ya ce, wannan shiri na Samar da kiwo ga mata shiri ne da suka shirya da zimmar cigaba da cika alkawuran su Na Samar da abin yi ga al’ummar jihar musam­man mata da matasa don dogaro da kai.

Gwamnan ya bada tab­bacin cewar, gwamnatinsa za ta ci gaba da bada goy­on baya da tallafawa mata da masu karamin karfi don su zama masu dogaro da kai don su samu rayuwa mai inganci.

Ya ci gaba da cewar, “A kokarin mu Na gaganin mun cimma dabarun karni na majalisar dinkin du­niya, wannan gwamnatin ta mu mun dukufa matuka don ganin mun cimma na­sarar yaki da talauci da sa­mar da aikin yi a tsakank­anin mata, matasa da masu karamin karfi”.

Ya kara da cewar, “ kamar yadda kuka sani ne cewar, ta kaddamar da shirin ko ta kwana kan harkokin Ilimi musamman ilimi a matakin farko don kara farfado da shi tare kuma kara inganta shi don kawar da jahilci a tsakank­anin matasa manyan gobe, haka kuma mun kara daura damarar tallafawa mata shi ya sa ma a yanzu muka ba su awakai don kiwata su da zimmar kawar da talauci a tsakanin su.

“Don haka zamu ci gaba da hada kai da dukkan kungiyoyin da ke da kudi­rin ciyar da al’umma gaba da kuma dukkanin masu ruwa da tsaki dake jihar don ciyar da al’ummomin mu gaba”.

Ya ci gaba da cewar cikin adadin awakai 1,780 da za mu rarraba ga mata 890 a dukkannin fadin jihar an dauko mata biyar-biyar ne kowace mazaba 178 dake Jihar ne kuma kowace mace an hada mata taure ne da akuya.

A cewarsa hikimar sa­marwa matan jinsin awakai don kiwatawa shine, a cikin karamin lokaci ne awaki kan iya haifuwa wadda in Allah yaso babu bata loka­ci za su iya tara musu garke don biyan bukatun rayuwa cikin sauki.

Tun farko da ta ke

jawabi kwwmishina a ma’aikatar mata a Jihar, Hauwa Bah Abubakar ta yabawa Gwamna Mai Mala ne bisa ga kokarinsa na sa­marwa da mata da matasa abin yi don dogaro da kai wadda kuma babban abin a yaba be.

Ta kara da cewar, wan­nan shiri na samarwa mata da matas a a in yi tabbatacce ne zai yi matukar rage zogi da irin kalubalen da aka fuakanta kan rikicin Boko Haram da matsar cutar mashako (Covid-19) da Ji­har ta yi fama da shi a baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *