Hobbasa: Kamfanin BOSKA ya yi wa majiyyata gata a Kano

Tura wannan Sakon

Danjuma Labiru Bolari, Daga Gombe

A kokarin da kamfanin Dexa Medica masu yin Boska keyi na duba lafiyar mutane a ranar Asabar din da ta gabata 20 ga watan nan na Agusta kamfanin ya gudanar da aikin jinya kyauta ga al’ummar cikin birnin Kano a unguwar Hausawa dake kan hanyar gidan Zoo.

A jawabin sa ga jama’ar da suka ci gajiyar shirin kamfanin na Dexa Shugaban shiya na kamfanin na yankin arewa Ayodele Opowowe, cewa ya yi kamfanin ya ware wannan ranar ce dan taimakawa jama’a masu larurar gani da masu fama da wasu kananan cututtuka da za’a yiwa aikin ido a basu glass da magunguna kyauta.

Ayodele Opowowe, yace kafin wannan rana sun ji ra’ayoyin mutane kan irin matsalar su shi yasa a wannan karo suka shirya taron a unguwar Hausawa a birnin kano, dan a duba lafiyar idanun su a basu magunguna da glass kyauta.

Yace daruruwan mutuane suka ci gajiyar shirin Inda yace shirin zai ci gaba a sauran jihohin kasar nan, inda a ranar juma’a mai zuwa za su gudanar da irin wannan aiki a jihar Bauchi arewa maso gabas na Najeriya.

Ya kuma ce dalilin ware wannan rana dan duba lafiyar idanu kyuata da sauran cututttuka, shi ne suna so ne suji daga kwastomomin su da suke amfanin da maganin su na Boska sannan su ga kuma ta yadda za su taimaka musu a jihohi 7 na fadin tarayyar kasar nan a cikin wannan shekara ta 2022.

Ya kuma kara da cewa daruruwan mutane ne a ciki da wajen garin Kano, magidanta yan kasuwa da sauran al’ummar gari har ma da matafiya ne suka ci gajiyar shirin nasu.

Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin da suka hada da Patience Solomon da Rose Oko da Amina Attahiru da Musthapha Aliyu, sun yabawa kamfanin ne sannan suka yi Kira da cewa su fadada shirin daga kwana daya zuwa kwanaki uku domin kara taimakon al’umma musamman marasa galihu.

Sannan suka kara godewa kamfanin bisa wannan kokari na su na duba lafiyar idanu da bada tabarau gami da magunguna kyauta a wannan rana da suka ware ta musamman ta ranar Boska Day campaign free for health care services da cewa ya kamata gwamnati ta bai wa kamfanin lambar yabo domin matsalar ido ita ce ke damun mutane da dama kuma basu da yadda za suyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *