Hobbasa: Shugaban majalisar dokokin Bauchi ya tallafa wa ilimi

Tura wannan Sakon

Jamilu Barau daga Bauchi

Kakakin Majalisar Dokokin jihar Bauchi, Alhaji Abubakar Y Suleiman ya yi kira ga al’umma daban-daban na jihar da su hada kai su tsara dabarun inganta ilimi da ci gaban kasa baki daya. Suleiman, ya bayyana hakan ne a yayin taron shekarashekara karo na 2 na kungiyar al’ummar Tiffi, domin ci gaban ilimi wanda ya gudana a makarantar firamare ta Tiffi da ke Ningi.

Shugaban majalisar ya bayyana cewa, kokarin da al’ummar Tiffi suke yi na bunkasa ilimi da ci gaban al’umma abin yaba wa ne kuma ya bukaci sauran al’ummar karamar hukumar Ningi da ma jihar baki daya da su yi koyi da su.

A cewarsa ilimi shi ne kashin bayan kowace al’umma kuma Tiffi ta yi fice a shekaru da dama a fannin ilimi da hadin kai domin haka ne ya sa ‘ya’yan yankin suka yi fice a kowane fanni na rayuwa a fadin kasar nan.

Kakakin majalisar ya kara da cewa, nasarorin da kungiyar ta samu ya burge shi matuka musamman yadda suka yi daidai da manufofinsa na bunkasa ilimi da kuma taimaka wa marasa galihu a mazabar.

“Abin da kungiyar al’ummar Tiffi ke yi ta hanyar bayar da gudummuwar hadin kan al’umma tamkar rage nauyi ne a kan gwamnati wanda zai jawo hankalin gwamnati cikin gaggawa. Kada mu nade hannunmu mu jira gwamnati ta yi komai, a matsayinmu na al’umma muna da rawar da za mu taka wajen kyautata rayuwarmu.

“Na bayar da gudunmawa ga kungiyar a bara, kuma a bana na ninka ta. Haka zan ci gaba duk shekara in Allah ya yarda.” In ji shi. Da yake jawabi tun farko, Sakataren kungiyar, Alhaji Hassan Mohammad ya bayyana cewa, an kafa kungiyar ne domin magance kalubalen ilimi da al’umma a Tiffi.

Ya bayyana irin ayyukan da kungiyar ta yi masu da suka hada da taimakon kudi ga Hobbasa: Shugaban majalisar dokokin Bauchi ya tallafa wa ilimi marasa galihu, ayyukan da suka shafi al’umma da biyan kudin makaranta ga ‘ya’ya maza da mata da dama na al’ummar da ke karatu a manyan makarantun kasar nan.

Alhaji Hassan ya yabawa shugaban majalisar bisa yadda ya damu da halin da al’ummarsa ke ciki da irin gudunmawar da yake bai wa kungiyar akai-akai. Muhimman abubuwan da taron ya kunsa sun hada da jawabai daga fitattun ‘ya’yan karamar hukumar Ningi da gabatar da kyaututtuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *