Hukumar askarawan Nijeriya ta ja kunnen Sheikh Gumi -A kan kalamansa

Sheikh Gumi
Rundunar sojin Najeriya ta gargadi babban malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Ahmad Gumi da cewa ya iya bakinsa kan irin kalaman da yake yi a lokacin ziyarar da yake kai wa sansanonin ‘yan bindiga a wasu sassan kasar.
Wata sanarwa da daraktan sashen watsa labarai na rundunar Birgediya Janar Mohammed Yerima ya fitar a ranar Talata da maraice ta ce, a yayin da rundunar ba ta son samun wani sabani tsakaninta da Sheikh Gumi, amma tana son bayyana cewa rundunar sojin Najeriya ba ta tura dakarunta bakin aiki kan bambancin addini.
Rundunar sojin ta yi wannan gargadi ne sakamakon wani bidiyo da ya yadu da ke nuna Sheikh Gumi a wata ziyara da ya kai wa ‘yan bindiga a cikin daji, yana ce musu yawancin sojojin da ke kai musu hare-hare ba Musulmai ba ne.
“Don haka muna rokon Sheikh Ahmed Gumi da masu irin ra’ayinsa da su kame kansu kar su shigar da rundunar soji mai matukar kima cikin lamarin da zai zubar mata da daraja.
“Rundunar sojin Najeriya tana ci gaba da zama abar alfaharin kasar da kuma kare mutuncinta. Kalaman da za su bata kima da darajar rundunar sojin Najeriya ba rikici kawai za su jawo ba har husuma za su tayar a tsakanin dan Najeriya,” a cewar sanarwar.
Ta kara da cewa rundunar sojin na ayyukanta cikin taka tsan-tsan da bin dokokin da aka kafa ta a kai, da girmama hakkin dan adam ba tare da nuna wariya ba“Don haka babban abin kunya ne a ce wani malamin addini ya dinga bata ta da gangan a idon duniya.”
A karshe, sanarwar ta bai wa malaman addinin shawarar yin taka tsan-tsan a yayin da suke bayyana ra’ayoyinsu, da bai wa tsaron kasa muhimmanci, musamman a wannan lokaci mai tsanani da dakarun tsaro suke kara zage damtse don shawo kan matsalolin da kasar ke fuskanta.
“Abin da dakarunmu ke bukata shi ne goyon bayan al’umma don yin aikinsu yadda ya dace,” kamar yadda sanarwar ta fada.