Hukumar FRSC shiyyar Bichi, ta yi alwashin inganta aiki -Saboda Kirsimeti, sabuwar shekara

Daga Jabiru Hassan
Kwamandan shiyyar Bichi na hukumar Kare hadurra ta qasa watau FRSC Hassan Rafi Yeldu yace, dogarawan da za su qara qoqari, wajen ganin an gudanar da bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara cikin nasara ta hanyar ci gaba da wayar da kan direbobi da hanyoyi amfani da ababen hawa kan hanyoyin mota.
Ya yi tsokacin ne yayin da wakilinmu ya ziyarci ofishin shiyyar, inda ya sanar da cewa, da yardar Allah, za’a gudanar da wadannan bukukuwa lafiya da nasara duba da yadda dogarawan sa suke aiki tukuru domin fadakar da direbobin motoci da masu ababen hawa har ma da fasinjoji muhimmancin bin dokokin hanya.
Malam Hassan Rafi Yeldu ya kuma bayyana cewa hukumar kiyaye haddurra ta kada tana aiki a dukkanin sassan wannan kasa domin tabbatar da cewa, ana yin tafiye-tafiye bisa bin qa’idojin tukin ababen hawa da kuma bin dokokin hanya wanda hakan ya taimaka sosai wajen raguwar hadurra a wannan qasa bisa alqaluman da hukumar me fitarwa duk qarshen shekara.
Ya kuma nunar da cewa, mafiya yawan hadurran da ake yi kan hanyoyin mota suna faruwa ne ta dalilin tuqin ganganci da yawan gudu da kuma lodin da yafi karfin ababen hawa, yace hakan ce ta sanya suke aiki sosai wajen fadakar da direbobi kan illolin tukin ganganci tare da jaddada cewa, ana bin qa’idojin tukin da na hanyoyin mota.
Haka kuma kwamandan ya ce, akwai alaqa mai kyau tsakanin hukumar ta FRSC shiyyar Bichi da dukkanin jami’ai masu sanya kayan sarki wanda ko shakka babu hakan ta sanya ake samun dukkanin nasarorin da ake buqata wajen rage hadurra a hanyar kan zuwa Katsina dama qasashe maqwabta.
Daga qarshe, Hassan Rafi Yeldu ya shawarci fasinjoji da su riqa qoqarin hawa mota a cikin tasoshin mota domin tabbatar da cewa, sun san daga inda suke, sannan ya yaba wa qungiyar direbobi ta NURTW na wannan shiyyar saboda kyakykyawar fahimtar juna da ake da ita tsakanin su da hukumar