Hukumar NITDA ta ja hankalin matasa kan samun horo

Hukumar NITDA ta ja hankalin matasa kan samun horo

Hukumar NITDA

Tura wannan Sakon

Daga Zainab Sani Shehu Kiru

Hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa, (NITDA) ta bukaci ‘yan Nijeriya da su nemi shirinta na horar da su kan bunkasa manhajar kwamfuta (NITDA Debelopers Group, NDG a turance.

Rahoton ya bayyana cewa, hukumar ta ce shirin zai kasance karkashin kulawar Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani na daga cikin kokarin sanya Nijeriya ta zama cibiyar fasahar zamani a Afirka baki daya.

NITDA ta sanar da shirin horas da masu kirkirar manhajoji miliyan daya a fannoni daban-daban na bunkasa aikace-aikace dama tattalin arziki. A Sanarwar da khugabar harkokin kamfanoni da hulda ta waje NITDA, Mista Hadiza Umar ta fitar a ranar Asabar, ta ce, aikin wanda za a gudanar ta hanyar reshen NITDA da cibiyar National for Artificial.

Darakta janar na NITDA, Kashifu Inuwa CCIE ya umarci NCAIR da ta gudanar da shirin a karkashin jadawalin aiki na tsawoyi 24/7 a cikin cibiyar gami da shirin horon da zai samar da matasa ayyukan yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *