Hukumar zabe, a soke takarar barayi –MSDG

Rijistar zabe: Shugabanni, a ja damarar ilmantar da jama’a –Gwamnati

Rijistar zabe: Shugabanni, a ja damarar ilmantar da jama’a –Gwamnati

Tura wannan Sakon

Jabiru A Hassan, daga Kano

Kungiyar tabbatar da shugabanci nagari watau Mobement For the Support of democracy and good gobernance” (MSDG) ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC da ta haramtawa dukkanin wadanda suke da laifuffukan almundahana da dukiyar kasa takara a zaben 2023.

A cikin wata takarda da ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Alhaji Alhaji Abubakar Shehu Usman kuma aka rarraba wa manema labarai a Kano, kungiyar MSDG ta ce, duk kasar da take da shugabanni masu satar dukiyar al’umma bata ci gaba, sannan ba za’a sami adalci a shugabanci ba.

Kungiya tana kira da babbar murya ga hukumar zabe da ta haramtawa dukkanin wadanda suke da shari’o’i a kotuna da hukumomin yaki da cin hanci watau ICPC da EFCC ta yadda kasar za ta sami daraja da mutunci a tsakanin kasashen duniya”. In ji sanarwar.

A karshe, kungiyar ta sanar da cewa, ta shirya tsaf domin fara wani gangami na neman soke takarar dukkanin wadanda suke da shari’o’i a kotuna da hukumomin yaki da cin hanci ta yadda za a hada hannu wajen tsabtace shugabanci a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *