Ibtila’in ambaliya: Shugaban karamar hukuma Misau ya rarraba kayayyankin tallafi

Tura wannan Sakon

Jamilu Barau Daga Bauchi

Shugaban karamar hukuma Misau, Alhaji Abubakar Ahmad (Garkuwan Misau) ya bayar da tallafi ga wadanda ibtila’in ya same su a yankin Akuyam ta karamar hukumar Misau.

A makon da ya gabata ne ambaliyan ruwa ya rusa gidajen al’umma tare da asarar rayuka da amfanin gona, al’umma da dama a karamar hukumar Misau sa sauran sassan jihar Bauchi.

A yunkurin sa, shugaban karamar hukuma Misau, Alhaji Abubakar Ahmad Garkuwan Misau ya tallafa wa wadansu daga cikin wadanda ibtila’in ya same su a yankin Akuyam da kayan masarufi domin rage masu radadi.

Ibtila’in ambaliya: Shugaban karamar hukuma Misau ya rarraba kayayyankin tallafi Ya kuma jajanta masu tare da yi masu addu’a na ganin yadda ibtila’in ya same su, Allah ya mayar masu a mafificinsa Ya kuma bayyana masu cewa, hukuma ta yi bakin kokarinta domin kaiwa inda ya dace, domin tallafa masu tare da yaba wa gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammed da ya bayar da damar kafa kwamiti na musammam kan koke-koken ambaliyan ruwa.

Tallafin ya samu wakilcin shugaban sashen koke-koke na karamar hukumar Misau, Alhaji Ladan Yarima (Barayan Misau) da tawagarsa inda ya mika sakon kai tsaye zuwa ga sarkin Akuyam, Alhaji Adamu Ibrahim Basal tare da kansila mai wakiltan mazabar Akuyam Alhaji Garba Babayo Akuyam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *