Idan masalaha ta gagara, ba na tsoron bugawa da kowa -Bala Mohammed

Idan masalaha ta gagara, ba na tsoron bugawa da kowa -Bala Mohammed
Tura wannan Sakon

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, wato daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a jam`iyyar PDP a Najeriya, ya ce da so samu ne zai so a ce sun cimma maslaha a tsakanin junansu wato `yan takara daga arewa, amma idan ta gagara baya fargabar shiga a yi zaben fidda gwani a tsakaninsu.

Gwamnan yana mai da martani ne ga matakin da takwaransa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, wanda ya ce maganar sulhu ta cije, kuma bai yarda da wata kuri`ar da wasu dattawa suka kada karkashin jagorancin Janar Ibrahim Babangida mai ritaya ba, inda suka zabi Sanata Bala Mohammed da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Gwamnan ya ce,” Idan an ce sulhu ya kakare, to ko me kakarewar dai an fito da sakamako, to amma duk da haka tun da ya kakare to ba wanda ya ke tsoron shiga takara, ni ban taba jin tsoron mutane ko kuma dan takara ba.”

Sanata Bala Mohammed ya ce duk wanda zai fito ya yi takara sai ya ci gaba, to amma sun gode wa dattawan arewa da suka yi musu sulhu, kuma sun ce duk wanda bai yarda ba yana iya zuwa ya ci gaba da neman takararsa.

Gwamnan na Bauchi, ya ce sai da suka cewa gwamna Tambuwal su je Minna, ya ce ba zaije ba, to da yake babban mutum ne ba wanda zai yi masa dole, to amma su sunyi alkawari cewa ba za a ji suna ce-cekuce da shi ba.

Ya ce,” Wannan abu ba wai abin fada ba ne, an riga an wuce wajen, don ya ce zai ci gaba da da neman fafatawa muma kuma zamu ci gaba amma da goyon bayan dattawan arewa dama mutanen arewa.”

Sanata Bala Mohammed ya ce la’akari da cewa su shiga takara kawuna a rabe zai iya janyowa arewa matsala, shi yasa suka ce gara su hada kai don su tafi kaifi daya amma abin ya ci tura.

Gwamnan na Bauchi ya ce abin da suka yi ba siyasa ba ce girmamawace ta zumunci don a kai ga gaci.

Ya ce abin da Janar Ibrahim Babangida mai ritaya, ya yi, ya yi ne don ya inganta adalci a tsakaninsu, saboda su muka bashi wuka da nama suka ce a fidda daya a tsakaninsu su kuma zasu bi duk wanda aka fitar.

“To ban san inda maganar son zuciya ta fito ba, don ko da aka kiramu aka ce ni da Bukola Saraki ne muka haye, wadanda suka yi zaben sun ce mu din ma mu ci gaba da tattaunawa kuma sauranma in suna so za su ci gaba” inji shi. Ya ce ba dai-dai ba ne a watsa wa dattawan da suka shiga tsakanin kasa a ido a ba, wannan bai ji dadi ba.

Tun da farko gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ne ya ce sun kasa cimma matsaya kan dan takarar da za su mara wa baya a tsakanin wata hadaka ta mutum hudu da suka kafa don daidaitawa wajen fitar da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

Gwamnan ya ce a yanzu babu batun maslaha ko kuma wani ya janye wa wani a tsakanin masu neman takarar. Gwamnan ya ce kafin wannan lokaci an yi tunanin tsakaninsa da Sanata Bukola Saraki da gwamnan Bauchi Bala Mohammad da Muhammad Hayatudeen da duk ke neman tikitin takara a inuwar PDP na iya maslaha a tsakaninsu.

Sai dai lura da yadda abubuwa ke tafiya kowa kawai tashi ta fisshe shi. Kafin wannan barakar ta kunno kai bayanai sun ce ‘yan takarar hudu sun so su fadada yunkurin nasu zuwa kasa baki daya a maimakon yankin arewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top