Ilimi: Matasan Gyadi- Gyadi Arewa sun yaba wa Habu PA

Alhaji Abubakar Zakari Mohammed Habu P.A
Daga: Ahmad Suleiman, Kano
An yaba wa shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Abubakar Zakari (Habu PA) saboda kwazonsa na habaka harkokin ilimi a karamar hukumar.
Wannan yabo ya zo ne daga bakin shugaban kungiyar ci gaban matasa na Gyadi-Gyadi Arewa, Malam Usman Ahmad ganin yadda aka samar da makarantar sakandaren mata ta kimiya a Ja’oji kwatas.
Ya ce, kawo makarantar Ja’oji kwatas ba karamin alheri ba ne ga al’ummar wannan yanki da kuma ci gaban ilimin mata a wannan jiha ta Kano.
Ya kuma yi kira ga shugaban karaman hukumar da ya yi kokari wajen ganin an zagaye wurin zuba shara da yake kan titin Zariya da ke jikin kantuna Ja’oji kwatas wacce hanya ce ta zuwa wannan makaranta da aka bude.