Ilimin mata yana bunkasa a Kano –Bincike

Ilimin mata
Daga Jabiru Hassan
A jihar Kano, binciken da wakinmu ya gudanar ya nuna cewa, ilimin ‘yammata yana samun ci gaba sosai a dukkanin makarantun da ake dashi a fadin jihar duk da irin kalubale da harkar ilimi ke fuskanta tun lokaci mai tsawo.
Bayan kammala hutun babbar Sallah, wakilinmu ya gudanar da wani bincike na musamman inda ya gano yadda gwamnatin jihar Kano take kokari wajen bai wa ilimi muhimmanci musamman ilimin mata duba da yadda abin yake da muhimmancin gaske.
Kusan dukkanin makarantun da Albishir ta leka suna cikin yanayi mai kyau duk da cewa, akwai bukatar a samar da karin gyare-gyare na dakunan kwanan dalibai da malamai da kuma kyautata yanayin bandakunan dalibai musamman a makarantun kwana.
Haka kuma binciken na wakilinmu ya gano cewa, gwamnati ta yi namijin kokari wajen samar da kwararrun malamai da ke koyarwa wanda hakan ta sanya duk inda aka je za a ga cewa, ana karatu bias kwazo da tarbiyya ba tare da wata matsala ba.
Bugu da kari, mafiya yawan dalibai da malamai da sauran ma’aikatan da suka zanta da wakilinmu sun yaba wa gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda kokarin da gwamnatin sa ke yi wajen bunkasa ilimi a jihar Kano musamman ilimin mata.
Sannan wajibi ne a jinjina wa babbar sakatariya a ma’aikatar ilimi ta jihar Kano watau, Hajiya Lauratu Ado Diso saboda jajircewar da take yi kan harkar bunkasa ilimi da tsayawa wajen magance duk wata matsala da take ciwa ilimi tuwo a kwarya.
Dangane da kula da makarantun gaba da firamare, ba za’a manta da Dokta Bello Shehu ba musamman yadda yake ta kokari wajen tabbatar da cewa, dukkanin makarantun ban ‘yan sakandare na jihar Kano suna tafiya cikin nasara, wanda kuma hakan ta sanya kwalliya take biyan kudin sabulu a dukkanin makarantun jihar Kano.
Sai dai kafin in kammala rahoton, akwai bukatar sake bai wa dakunan sakandiren ‘yammata ta Kwa umarnin komawa makarantar da kwana saboda yawan da suke da shi kuma ababen hawa suna masu wahala wanda wasun su dole tasa suke tafiya mai nisa a kasa wadansu kuma dole suke zama a gida.
Komawa da dalubai cikin makarantar zai sanya a ci gaba da karatu a wannan makaranta ta ‘yammata da ke Kwa duba da yadda bincike ya nunar da cewa, makaranta ce mai tsohon tarihi wadda ta yaye dalibai mata fitattu kuma wadanda a yau suke bayar da gagarumar gudummawar su wajen ci gaban kasar nan game kuma kwararrun malamai da ake da su a gurin.