Illolin da magungunan taƙaita haihuwake yi wa mata

Tura wannan Sakon

Daga Wakilinmu

A 2001, ma’aikaciyar da ke zaune a birnin Boston, kamar sauran miliyoyin mata a fadin duniya, na shan kwayoyin barin taz­ara tsakanin haihuwa.

Amma ba kamar sauran matan ba, Banessa ta fuskanci wata illa da ke tattare da amfani da irin wadannan magungunan – gudan jinni, wanda ta ce ya sauya rayuwarta har abada.

“Ina hawa bene sai kawai na ji numfashina ya dauke,” a cewar Ban­essa.

“Ban taba jin irin haka ba sai na yi kokarin jan numfashi sosai.”

Duk da halin da ta tsinci kanta Banessa ta je aiki amma ta tashi da wuri don ta je asibiti.

“Sun ba ni wata na’ura da za ta taimaka wajen bude hanyoyin iska a jikina.

“Na dan ji sauki kuma numfashin ya daina yi min wahala. Sun dauki ho­ton huhuna sai suka ce sun ga wata in­uwa a ciki babu mamaki limoniya ce.”

Amma washegari sai asibitin suka sanar da Banessa cewa ba limoniya ba ce amma za su sake yi mata gwaje gwaje.

Sai da aka kwashe wata guda ba ta samu ganin likita ba, ga shi num­fashi na kara yi mata wahalar yi.

“Rannan ina aiki a gida, ina wanke kayana ina ta hawa da sauka a bene sai numfashina ya fara dauke­wa, sai na zuge zif din rigata. Nan na fadi kasa a dakin girki saboda na kasa shakar iska.

“Jikina babu inda ba ya ciwo, cikina, kirjina da hannuwana duk suka rika ciwo. Na dauka bugun zuci­ya zan samu.”

Banessa ba ta je asibiti ba amma ta buga wa likitanta waya, inda aka ba ta shawarar ta je asibitin cikin gag­gawa.

“Washe gari, na je na ga likita na gaya mata yadda nake ji sai ta duba ni. Daga nan ne ta tura ni babban asibiti don a yi min gwaje gwaje sosai.

“Na je aka jona ni a jikin na’urori, gaba daya na shiga rudani.”

“An gano ashe ina da wani katon gudan jini a kirjina, kuma ya fara far­fashewa har mamaye mafi yawan hu­huna.”

Kwanan Banessa biyu a asibiti ka­fin a sallame ta amma mako biyu ta kwashe tana jinya.

Ta ce likitoci sun gaya mata mai yiwuwa sauya kwayoyin hana daukar ciki da ta yi ne ya janyo mata wannan gudan jinin.

“An shaida min cewa da na kara kwana guda kafin in zo asibiti da na rasa rayuwata,” a cewarta.

Dama ana yawan samun gudan jini a mata masu shan kwayoyin takaita haihuwa?

A cewar Hukumar Insorar Lafiya ta Burtaniya NHS, a kasar, ‘ya dan­ganta tsakanin mata biyar zuwa 2 ne ke samun gudan jini a cikin mata 10,000 da ke amfani da su a shekara.

NHS ta ba da shawarar cewa duk macen da ke cikin shakku ta tuntubi likitanta.

A fadin duniya, mata sama da mil­iyan 150 ne ke shan wadannan ma­gungunan kuma su ne suka fi shahara a Turai da Australia da New Zealand. Kuma su ne na biyu mafiya shahara a Afrika da Latin Amurka da Amurka.

Kwayoyin, kamar ko wane nau’i na tazarar haihuwa na da illolinsu ciki har da yawan fushi da sa kiba ko rama. Wadannan ne aka fi gani.

Amma akwai illolin da ba a cika gani ba kamar samuwar gudan jini wanda ke da hadari. Wannan hada­rin ya danganta ne da yawan sindarin da mace ke samu daga kwayoyin da shekarunta da yadda take gudanar da rayuwarta misali idan mai kiba ce ko kuma idan tana shan taba sigari.

Ba kowa ne ke samun gudan jini ba Kwayoyin na da sindarin oestrogen da aka samar a dakin gwaji ko proges­terone ko duka biyun.

“Sinadarin Oestrogen na janyo samuwar kwayaye a mahaifa, don haka idan kwayayen suka yi kwari sai su sakko zuwa mahaifa inda a nan ne ciki zai iya samuwa, a cewar Dakta Zozo, kwararriya a bangaren haihuwa a asibitin Stebe Biko da ke Pretoria a Afrika ta Kudu.

“Amma idan sinadarin oestrogen ya yi yawa sai ya bai wa kwakwalwa alamar haka, sai a samar da kway­aye,” a cewarta.

Dakta Nene ta yi bayanin cewa sinadarin progesterone na aiki ta han­yoyi uku ne; yana kara kaurin ruwan da ke bakin mahaifa don kada mani­yyi ya samu damar wucewa.

Sannan yana hana mahaifa rike jariri.

Haka kuma, yana tunkudo kwai ya biyo hanyoyin nan da ake kira “fallo­pian tubes” ya hadu da maniyyi a sa­mar da jariri.

“Don haka sinadaren biyu na aiki tare don hana samar da kwayaye da kuma zaman jariri a mahaifa,” a cew­arta.

Illolin shan wadannan kwayoyin da ake gani sun hada da tashin zuciya da amai da kara kiba da kumburin ciki da kuraje a fuska.

“Wasu kan ce sun samu raguwar sha’awa da ciwon kai da jin zafi a ma­mansu da yawan fushi,” in ji Dakta Nene.

“Yana da kyau a san abin da ke jawo wadannan illoli ,” in ji ta.

Jikin dan Adam na da sindaran da ke iya samar da gudan jini dai dai wa dai da. Amma idan suka hadu da irin wadannan kwayoyin sai hatsarin sa­mun gudan jinni ya karu a jiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *