Inganta tsaro bisa doron shariah: BUK, Majalisar Malamai sun shirya wa malamai bita

Daga Aliyu Umar
Majalisar malaman Nijeriya, reshen jihar Kano, da hadin gwiwar sashen Nazarin addinin Musulunci da shari’a, jami’ar Bayero sun shirya wa limaman jihar bitar kara wa juna sani, daga ranar Asabar 4 ga Satumba zuwa 5 ga Satumba, 2021.
Taron, wanda aka gudanar a babban dakin taro na Mahmud Tukur, a tsohuwar harabar jami’ar Bayero, takensa; ayyukan limamai da masu da’awa domin inganta tsaro bisa doron shariah, ya sami halartar limamai da manyan malamai, bisa jagorancin shugaban majalisar, shiyyar Arewa maso yamma, kuma shugabanta na jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil.
Da yake gabatar da jawabin maraba, a madadin shugaban jami’ar Bayero Kano, Farfesa Abdullahi Sule Kano, ya fara mika sakon fatan alheri ga mahalarta taron daga shugaban jami’ar. Farfesa Abdullahi Kano, ya yi waiwaye kan gudunmowar limamai da malamai suka bayar a zamanin mulkin Shehu Usmanu Danfodiyo, inda ya ce, tsantseni da takatsantsan, da gudun duniya, su suka jawo nasarar da da’awa ta yi, a zamanin daular Usmaniyya.
Ya ce, sarkin Musulmi Attahiru ya ki yi wa ‘yan mulkin mubaya’a, ya ja jama’arsa suka doshi Bauchi, a kan hanyarsu ta zuwa gabas, sai Turawa suka katse masa hanzari, suka kashe shi.
Shi kuwa Sarkin Musulmi Bello, shi ya shuka yalon nan da ake kira yalon-bello, domin ciyar da iyalinsa gudun kada ya shiga hakkin talakawa. Tun da farko, babban mai jawabi, Dokta Yahaya Tanko, ya gabatar da makala mai taken, ‘Gudunmowar malamai wajen tarbiyantar da al’umma’, inda ya yi bayani kan ma’anar kalmar malami, da tushenta, tare da yin kira ga Limamai, malamai da su sifantu da sifofin malamai guda biyu (1) gaskiya (2) amana. Ya ce, sifantuwa da yin gaskiya, da rikon amana, hakan shi zai kare masu martaba, da daukakar da suke da ita cikin al’umma.
Dokta Yahaya Tanko, ya kara da cewa, ‘muddin limamai da malamai suka doshi hanyar wulakanta kai, ilimi da shugabanci za su shiga garari, ganin cewa, limami shi ne shugaban jama’a, ba shugaban kwamitin masallaci ba, wanda yake karkashin limi A nasa jawabin, mai taken gudunmowar limamai wajen yin da’awa ko kira zuwa ga tafarkin gaskiya, Dokta Mu’azzam Khalid, ya ce, kasancewar addinin Musulunci bai yi karo da dabi’ar dan’adam ba, shi ya sa Ubangiji SWT fiye da sau 215 ya ambaci da’awa ta yin kira zuwa ga addinin gaskiya.
Shi ma ya yi karin haske a kan ma’anar kalmar da’awa, a harshe da kuma ma’anar kalmar a addinance, inda ya kara da cewa, liman shi ne shugaban jama’a ko al’umma, a saboda haka, shugaban kwamitin masallaci shi ma a karkashin liman yake.
Da yake gabatar da tasa makalar, mai taken, ‘Rubutun Ajami ko rubuta harshen Hausa da bakaken Larabci, Dokta Aminu Isma’il Sagagi, ya yi magana kan bukatar da ke akwai ta a farfado da rubuta Hausa da bakaken Larabci ko Ajami, ganin cewa, fiye da kashi 95 cikin 100 za su iya karatu da shi.
Ya ce, ana yi wa Ajami kirari da, ‘Ajami gagara mai shi, wadansu kuma su ce, mai abu da abinsa. Daga nan ya shawarci mahukunta da su karfafa rubutun Ajami wajen gayyata da allunan tallace-tallace, da alluna masu nuna alamun hanya, ko shiga gari da makamantan haka, domin bunkasa harshen Hausa, da daukaka addini.
Dokta Ahmad Sa’id Dukawa, shi ya yi wa makalar Dokta Yahaya Tanko karin bayani ko ta’aliki.