Ingila ta gamu da cikas mafi muni -Cikin shekaru 100

Tura wannan Sakon

Ingila ta gamu da cikas kashi mafi muni -Cikin shekaru 100

A karon farko cikin kusan shekaru 100, Ingila ta sha kashi mafi muni a gidanta a fafatawar da ta yi da Hungary wadda ta zazzaga mata kwallaye 4-0 a gasar Nations League  ta Kasashen Turai.

Tun shekara ta 1928 rabaan da wata kasa ta yi wa Ingila irin wannan cin a gidanta, inda a wancan lokacin ta sha kashi a hannun Scotland da kwallaye 5-1.

kwanaki 10 da suka gabata, Hungary ta doke Ingilar da ci 1-0 a Budapest.

Tuni dai kocin tawagar Ingila Gareth Southgte ya fara shan matsin lamba, inda ake ganin cewa, ya kama hanyar kafa mummunan tarihi a matsayinsa na mai horas da kasar.

Yanzu haka yana da sauran wasannin da za su zame masa zakaran gwajin dafi gabanin soma gasar cin kfoin duniya a Katar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *