Ingila ta ja ragamar rukuni na hudu -Bayan doke Czech

Ingila ta ja ragamar rukuni na hudu
Tawagar kwallon kafa ta Ingila ta yi ta daya a rukuni na hudu, bayan da ta doke Jamhuriyar Czech 1-0 a gasar cin kofin nahiyar Turai ranar Talata.
Dan wasan Manchester City, Raheem Sterling ne ya ci mata kwallon, kuma na biyu a gasar cin kofin nahiyar Turan wato Euro 2020.
Ingila wadda ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe za ta kara da duk wadda ta yi ta biyu tsakanin Faransa ko Jamus ko Portugal ko kuma Hungary a Wembley.
Tun da fara karawar Sterlin ya buga kwallo ta bugi turke, kafin ya ci wa Ingila kwallon da take bukata, ta kuma hada maki bakwai a wasa uku a rukuni na hudun.
Bukayo Saka yana da hannu a kwallon da Ingila ta zura a raga, kuma dan wasan Arsenal din ya taka rawar gani a fafatawar.
Harry Kane ya nemi raga, amma golan jamhuriyar Czech, Tomas Vaclik ya hana kwallo shiga gidan kifi, shima mai tsaron ragar Ingila, Jordan Pickford ya hana Tomas Holes ya ci kwallo.
Bayan da suka huta suka koma zagaye na biyu dan wasan Ingila, Jordan Henderson ya ci kwallo, amma alkalin wasa ya ce an yi satar gida.
Tawagar Ingila za ta fafata da wadda ta yi ta biyu a rukuni na shida ranar Talata 29 ga Yuni a Wembley.
Rukuni na shida zai buga wasanninsa na karshe ranar Laraba 23 ga watan Yuni tsakanin Jamus da Hungary da na hamayya tsakanin Portugal mai rike da kofin nahiyar Turai da Faransa mai rike da kofin duniya.