Iyaye, a kara bai wa ‘ya’ya damar samun ilimi –Aliyu

Tura wannan Sakon

Daga Musa Diso

A ranar Lahadi da ta gabata, daya daga cikin yara 20 da suka yi saukar karatu a makarantar Halakatu Tahfizul Kur’an da ke masallacin Alfur’kan kan titin Alu Abenue, a karamar hukumar Nassarawa, Aliyu Jibrin Ala, ya roki iyayen yara da su kara bai wa ’ya’yansu kwarin guiwar samun ilimin addini da kuma na zamani domin gudanar da rayuwarsu mai albarka.

Ya yi bayanin ne bayan kamala saukar karatu da makarantar ta yi inda aka yaye dalibai 20, mata da maza tare da jadda cewa, idan har yara za su ci gaba da samun kulawa ta musamman kan neman ilimi da iyayensu ko shakka babu za a sami al’umma tagari kuma mai albarka.

Aliyu Jibrin ya sanar da cewa, neman ilimi abu ne mai muhimmanci, don haka, yana da kyau iyaye su kara bai wa yaransu cikakkiyar damar samun ilimi mai nagarta duk da irin dawainiyar da ke tattare da nemansa.

Ya kuma shawarci ’yan uwansa yara da su kasance masu biyayya ga iyayensu da malaman makarantarsu.

Daga karshe ya yi amfani da wannan dama wajen yaba wa malaman da sauran abokanan karatunsa bisa yadda aka hada hannu wajen ganin sun sami damar saukar karatun Alkur’ani a matsayin su na masu tasowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *