Jagorancin Barden Bichi ya kyautata ci gaban Bichi –Bincikenmu

Alhaji Sani Mukaddas

Tura wannan Sakon

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Tarihin karamar hukumar Bichi ba zai taba mantawa da Alhaji Sani Mukaddas, ba domin komai ba domin shi ne ya zama zababben shugaban karamar hukumar har karo na biyu, da a zamanin sa ne karamar hukumar Bichi ta samu sauyesauyen ci gaba na tarihi da ya dada kawo bunkasar ta.

A tsawon shekarun da Alhaji Sani Mukaddas Barden Bichi, ya yi na jagorancin karamar hukumar Bichi ya kawo ci gaban da ya dada fito da matsayin bunkasar karamar hukumar a fannoni na ci gaba daban-daban kama daga harkar ilimi, gina al’umma musamman matasa maza da mata da kuma ci gaban harkar noma da kasuwanci da yin hanyoyi.

Wani babban al’amari shi ne a lokacin shugabancin Sani Mukaddas Barden Bichi ne gwamnatin jihar Kano a karkashin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta kirkiri karin masarautu a jihar Kano da Bichi ta rabauta da masarauta aka nada sarkin Bichi na farko daga zuriyar Marigayi Sarkin Kano Dokta Alhaji Ado Bayero inda aka nada dansa Alhaji Aminu Ado Bayero.

Wanda shi ne sarki na farko mai daraja ta daya da aka fara yi a Bichi sannan bayan an matsa da shi ya zama sarkin Kano, aka nada dan uwansa wanda shi ma da ne ga marigayi tsohon sarkin Kano mai martaba Alhaji Ado Bayero, Alhaji Nasiru Ado Bayero a matsayin sarkin Bichi na biyu.

Ga dukkan wanda yasan yanda karamar hukumar Bichi take a baya kafin zuwan shugabancin karamar hukumar da Barden ya yi zai tabbatar da yanda aka samu gagarumin sauyi na zahiri, musamman ma na yanda Bichi ta dada fadada da gine-gine da ayyuka da dama a fannoni daban-daban da yanzu ta kama hanyar zama babban birni bayan jihar Kano, wannan dama yana daga cikin manufar da gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya sa aka kirkiri karin masarautu a jihar Kano.

Tabbas al’ummar Karamar hukumar Bichi zasu cigaba da tuna Barden Bichi. Alhaji Sani Mukaddas a matsayin shugaba jagora dan siyasa mai kyakkyawar mu’amala daya kawo cigaba mai yawa kuma mai dorewa ga al’ummar Bichin a cikin tsawon shekakaru Uku-uku sau Biyu da yayi a matsayin zababben shugaban Karamar hukumar Bichi.

Wadannan muhimman nasarori da Barde ya sami ya same sune bisa irin.kulawa da aiki tukuru da bibiya da yake bisa kuma irin dinbin goyon baya da sahalewa da Gwamnan jahar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya bashi tareda hadin-kai daga Kwamishiman kananan hukumomi. Hon.Murtala Sule Garo.

Shi yasa kullum al’ummar Bichi a daidai lokacinda wa’adin mulkin Barde na zangonsa na karshe na Biyu ya kawo karshe suna cewa da ace akwai dama ta Barde ya sake Neman shugabancin zasu cigaba da bashi goyon baya amma duk da haka sunayi masa fatan.alkhairi da addu’ar samun babban rabo zasu kuma cigaba da bashi goyon baya a duk wata bukatarsa ta siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *