Jama’a, a bai wa tsarin hukumar kidaya goyon-baya -Nasiru Isa

Jama’a, a bai wa tsarin hukumar kidaya goyon-baya -Nasiru Isa

Hukumar kidaya

Tura wannan Sakon

Abubakar Garba Isa

Shugaban kidaya na kasa, Alhaji Nasiru Isa ya yi kira ga jama’ar jihar Kano da su bai wa hukumar kudaya ta kasa goyon baya. Da yake jawabi a dandalin baje koli da yake gudana karo na 43 a jihar Kano.

Shugaban hukumar ya yaba wa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Dokta Abdullahi Umar Ganduje a gurin shirya gagarumin ayyukan ci gaba da ya ganewa idonsa a cikin kankanin lokaci.

A jawabinsa, kwamishinan hukumar kidaya ta kasa, Dokta Sulaiman Isma’il ya yaba wa shugaban hukumar kidaya ta kasa da ya bayar a wajen dandalin baje kolin a jihar Kano. Dukkanin kwamishinan hukumar 36 sun sami halartar hakan ya nuna muhimmancinsa.

A nasa jawabin babban mai bai wa gwamna shawara a kan harkar kidaya, Alhaji Bashir.M. Baiwa, ya jinjina wa jihar Kano saboda kirkiro ofishin mai bai wa gwamnati shawara a kan harkar kidaya.

Haka kuma ya shawarci jama’ar jihar Kano da su tabbartar an kidaya su domin mu tabbatar da rike kambummu na jihar da tafi kowace jiha yawan jama’a a Nijeriya.

A jawabinsa, shugaban kasuwar baje kolin ta jihar Kano na riko a karkashin jagorancin Alhaji Ahmed Aminu ya godebwa hukumar kidaya ta kasa bisa muhimmancin da suka bai wa baje kolin ta jihar Kano karo na 43 da yake gudana wannan lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *