Jama’ar Borno sun yaba da gudunmawar kwalejin Tatari Ali –Rahoto

Tura wannan Sakon

Jamilu Barau daga Bauchi

Al’ummar jihar Borno sun yaba wa hukumar kwalejin kimiyya da fasaha ta Abubakar Tatari Ali da ke Bauchi (ATAPOLY) kan irin gudummawar da take bayarwa kan harkar ilimi da kuma gina al’umma.

Yabon ya fito ne daga bakin ko-odineto na hukumar raya yankin Arewa maso gabas na jihar watau NEDC, Injiniya Muhammad Umar yayin da yake jawabi a wajen taron bita da kwalejin tare da hadin gwiwar hukumar suka shirya a Maiduguri babban birnin jihar.

Injiniya Muhammad Umar ya ce, dole ne a yaba wa hukumar kwalejin musamman shugabanta, Dokta Alhaji Adamu Saidu saboda zakulo jajirtattu kuma hazikai cikin Mallaman kwalejin, domin bayar da gudummawa da nufin inganta harkar tsaro da zaman lafiya a tsakanin al’umma, musamman a jihar ta Borno da rikicin ta’addanci na Boko Haram ya lalata a shekarun baya.

Injiniya Muhammad Umar ya ce, irin taron bitar zai taimaka matuka gaya domin ganin an samu dorewar zaman lafiya a tsakanin al’umma da kuma kara masu karfin gwiwa duk da irin halin kakani ka yi na tsawon lokaci a dalilin rikicin ta’addanci na Boko Haram.

Taron bitar ya gudana karkashin jagorancin shugaban sashin ilimi mai zurfi na kwalejin, Dokta Muhammad Auwal tare da ‘yan tawagar sa, Mallam Musa Yakubu dakuma Mallam Faruk Aliyu dukkansu Mallamai a kwalejin Abubakar Tatari Ali da ke Bauchi.

Idan za ku iya tunawa, irin taron bitar an gabatar da shi a wadansu jihohi na yankin Arewa maso gabas da nufin inganta harkar tsaro da kuma zaman lafiya a tsakanin al’umma

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *