Jama’ar Kano, a bai wa rajistar zabe muhimmanci -Maiturare

rajistar zabe

rajistar zabe

Tura wannan Sakon

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Anyi kira ga matasa a kan su kula da da bayar da muhimmanci ga yin rijistar zabe,wanda ba zance ba ne na bambamcin jam’iyyar siyasa PDP ko APC zance ne na kishin jihar Kano da kasa kowa ya ta shi ya bayar da gudummuwa da za ta bayar da ma’ana akai domin samun nasara, Alhaji Dayyabu Ahmad Maiturare jigo a jam’iyyar PDP a Kano daga karamar hukumar Dala ya yi kiran.

Alhaji Dayyabu wanda kuma shine Galadiman Gado da masun Kano ya yi nuni da cewa, fiye da watanni 2 jagoran PDP Injiniya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce, akwai bukatar a tuntubi matasa a sanar da su muhimmanci yin rijistar zabe, kuma sun isar da sako nasa ga mutane kuma an yi iyakacin kokari an samar da cibiyoyi na koyawa matasa yanda ake yin rijistar ta na’ura mai kwakwalwa kuma an koyar da mutane da yawa sun tafi kasa cikin al’umma suna koyar da matasa.

Ya ce, abu ne mai muhimmanci ga gwamnatin jihar Kano ta jajirce wajen bibiya da sanya ido ga kwamitoci da aka yi na wayar da kai a kan yin rijistar, kuma gwamnati karfi gareta da za ta iya yin duk abin da ya kamata ta sanya kudi sosai a wayar da kai koda da daukar nauyin mutane ne su tsaya su yi.

Alhaji Dayyabu Ahmad Maiturare ya ce, ya kamata Gwamnati tasa a rika kwaroroto sosai a kafafen yada labarai a kan muhimmacin rijistar kuma ta dauki nauyin mutane su tsaya su yi ko da kudi a ba su yanda za su tsaya su yi kamar yanda ake lokacin zabe.

Daga karshe, Alhaji Dayyabu Ahmad Maiturare ya yi kira da al’umma su yi hakuri kar su sanya rashin amfana da gwamnati matsayin abin da zai sa suki yin rijistar da kuri’a ne ake kafa gwamnati da kuri’a ake sauya ta mutane su yi hakuri kar su ga cewa, ko gwamnati ta gaza yin wannan rijistar yi wa kai ne taimako kanka ne ka zabi wanda ya da ce da kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *