Jami’ar Amirka ta karrama shugaban AFAN

Dokta Farouk Rabiu Mudi

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Jami’ar Prowess da ke kasar Amirka ta karrama shugaban kungiyar manoma ta kasa, Dokta Farouk Rabiu Mudi da digirin girmamawa saboda gagarumar gudummawar da yake bayar wa ga ci gaban noma a Nijeriya.

A wani kasaitaccen biki da aka yi a babban dakin taro na jami’ar Legas, an bayyana Dokta Farouk Mudi a matsayin shugaba wanda yake kokari sosai wajen kawo managarcin sauyi a fannin noma domin wadata kasa da abinci kamar yadda manufofin gwamnati suke.

An shaida wa mahalarta bikin cewa, an bai wa shugaban kungiyar manoma ta kasa, Farouk Rabiu Mudi digirin girmamawa na (Honoris CAUSA) saboda irin gudummawar da yake bayarwa wajen bunkasa noma mai riba bisa shugabancinsa, tare da jaddada cewa, kungiyar AFAN tana daga cikin kungiyoyi da ake alfahari da su a Nijeriya”.

An kuma karrama sauran mutane irin sarkin noman Mambila, Alhaji Halidu da shugaban karamar hukumar Tsanyawa, Alhaji Kabiru Dumbulun da uwargidan gwamnan jihar Bayelsa, Madam Gloria Diri sai jakada Susan da shugaban hukumar kula da ma’aikata ta jihar Ogun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *