Jana’izar Sarauniyar Ingila 19 ga Satumba: Karbar bakuncin shugabanni zai bambanta-Mahukuntan Burtaniya

Jana’izar Sarauniyar Ingila 19 ga Satumba: Karbar bakuncin shugabanni zai bambanta-Mahukuntan Burtaniya

Jana’izar Sarauniyar Ingila

Tura wannan Sakon

Gwamnatin Birtaniya ta ce, ziyarar da shugabanin kasashen duniya za su kai kasar domin halartar jana’izar Sarauniya Elizabeth, zai bambanta daga kasa zuwa kasa, bayan rahoton da aka gabatar cewa, ba a bukatar shugabannin kasashen duniya su je kasar da jiragen su sai na haya.

Firayi minista Liz Truss ta ce, shirin karbar bakin shugabannin zai bambamta daga kasa zuwa kasa, dangane da abin da ya shafi tsaro da kuma hadarin da ake fuskanta, saboda haka za su gabatar da bayanai da kuma shawarwari ga ofisoshin jakadancin kowace kasa da ke Birtaniya.

Wannan matsayi na hukuma, ya biyo bayan sanarwar da wata kafar yada labarai ta gabatar, cewa, an bukaci shugabannin kasashen duniya da za su halarci jana’izar da su shiga jiragen fasinja, a yayin da za a sanya su a cikin motar bas da za ta dauke su zuwa wurin bikin da ke Westminster.

Matsayin na sanya shugabannin kasashen duniya a cikin motar bas ya haifar da cece-ku-ce, yayin da jami’an diflomasiya suka bayyana cewa, abu ne mai wahalar gaske.

Akalla manyan bakin da suka hada da shugabannin kasashe da Firayi ministoci 500 ake sa ran su halarci jana’izar a karshen mako. Wannan ita ce jana’iza mafi girma da za a yi a Birtaniya tun bayan ta Firayi minista Wisnton Churchill a shekarar 1965.

Ana sa ran jibge dubban ‘yan-sanda daga wajen birnin London domin aikin samar da tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *