Janye tallafin fetur:OXFAM ta nuna wa Nijeriya yatsa

Labarin kari kan farashin man fetur,kanzon-kurege
Tura wannan Sakon

Kungiyar ODFAM ta gargadi gwamnatin Nijeriya da ta kauce wa shawarar hukumar bayar da lamuni ta duniya IMF wajen gaggauta kara yawan harajin BAT da cire tallafin man fetur da kuma daina bambanta yadda ake sayar da kudaden kasashen ketare.

 Kungiyar ta bayar da shawarar daukar ingantattun matakai na kusa da na nesa wadanda za su tabbatar da kara yawan kudaden da gwamnati ke kashewa domin bunkasa rayuwar jama’a maimakon dakile kudaden da hukuma ke kashewa. Daraktan kungiyar a Nijeriya, Bincent Ahonsi ya ce, kara yawan kudaden harajin BAT da kuma cire tallafin man zai dada jefa ‘yan Nijeriya da dama cikin kangin talauci.

Kungiyar ta bayyana cewa, mutane biyu da suka fi kowa kudi a Nijeriya sun mallaki dukiyar da ta zarce na mutane miliyan 63 da ke fafutukar samun abin da za su ci.

Saboda matsayin kungiyar ta ce, ya dace Nijeriya ta mayar da hankali wajen kara wa attajiran kasar haraji da kuma karkata kudaden wajen gudanar da ayyukan raya kasa da suka hada da gina hanyoyi da samar da ruwan sha da gina asibitoci da tallafa wa manoma da kuma masu bincike a kan yadda za a inganta hanyar noma lura da yadda sauyin yanayi yake illa a duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *