Jarrabawar gwaji: Dalibai likitoci 439 daga ketare ba su ci ba

Osagie

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

Hukumar kula da aikin likitanci ta kasa ta ce likitocin da suka sami horo daga kasashen waje akalla 439 daga cikinsu suka faxi jarrabawar gwaji da za ta ba su damar yin aiki a Nijeriya.

Shugaban hukumar, Dokta Tijani Sanusi, shi ya bayyana haka a ganawar da ya yi da manema labarai a Lahadin da ta gabata, inda ya ce, likitocin da suka sami horo daga kasashen waje su 916 suka zauna jarrabawar, amma 477 kawai suka ci. A yayin da yake bayyana cewa, ana gudanar da irin jarra bawar a ko’ina a duniya.

Sanusi ya ce, babu kwararren da za a bari ya yi aiki a kasar da ba a nan ya yi karatu ba, sai idan ya ci jarrabawar. An gudanar da jarrabawar gwajin ta kwanaki 2 a ranakun 23 da 24 ga watan Nuwamban da ya gabata a asibitin koyarwa na jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto.

Makasudin shirya jarrabawar shi ne, tabbatar da cewa, duk likitan da ya yi karatu a wata kasa ya nuna kansa a matsayin wanda zai iya gudanar da aikinsa a Nijeriya.

Idan ya ci jarrabawar kuwa, za a ba shi lasisin da zai ba shi izini da damar yin aiki a Nijeriya na wucin gadi. Da lasisin ne waxanda suka karanci aikin likitanci a kowane fannni za su yi aiki na wucin gadi tsawon shekara guda, daga nan ne za a ba su cikakken lasisi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *