Kananan hukumomi 774 sai tsalle: Majalisun tarayya sun tabbatar da dokar cin-gashin-kai

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

Majalisar Dattawa ta kada kuri’ar amincewa da ‘yancin cin gashin kankananan hukumomi da majalisun dokokin jihohi da kuma bangaren shari’a a matakan jihohi.

Wannan na daga cikin tanade tanaden da ake yi wa kundin Duba shafi na 2 tsarin mulkin kasar gyaran fuska da zummar karfafa kananan hukumomin a matsayin matakan gwamnati na 3 bayan gwamnatin tarayya da ta jihohi.

Yanzu haka gwamnonin jihohi sun ki sakin mara ga kananan hukumomin domin gudanar da ayyukansu saboda yadda kundin tsarin mulkin da ake amfani da shi na shekarar 1999 ya ba su damar sanya ido a kansu.

Wannan ya sa gwamnonin ke yin dokoki yadda suke so na tafiyar da kananan hukumomin da kuma karbe masu kudaden da suke samu daga asusun tarayya a karkashin dokokin da suka yi na asusun hadin gwiwa.

Ita kuwa majalisar wakilai ta kada kuri’ar kin amincewa da bukatar bai wa shugaban majalisar Dattawa da na wakilai albashi har iya rayuwarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *