Kanawa, a mara wa gwamnatin Abba Kabir – Sani Dan-dila

Tura wannan Sakon

An bukaci mutanen jihar Kano da su bayar da cikakken goyan baya da hadin kai ga sabuwar gwamantin Abba Kabir Yusif ta Kano, da nufin samun damar sauke nauyin da Allah ya dora masa na tafiyar da jagorancin al’umar jihar baki daya.

Bayanin ya fito daga bakin Alhaji Sani Dahiru Dandila daga karamar hukumar Doguwa, yayin wata ganawa ta musamman da wakilin Albishir.

Ya ce, babu wani abu da ke cikin tafiyar ta wannan gwamnati da NNPP ta kafa a jihar Kano, da ya wuce kyautata wa al’ummar jahar baki daya.

Daya juya kan sha’anin harkar makarantu a jihar nan ya yi addu’ar tafi da tsarin lura da malaman makarantun bai daya ta fuskar biyansu kan lokaci, bisa amincewar gwamnatin ta Abbba Kabir.

Daga bisani Alhaji Sani Dahiru, Dan-dila ya yaba wa masu ruwa da tsaki da ke tafiyar da dukkam tsare-tsaren da ya wajaba a jami’yyar NNPP a kasa da ma jiha baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *