Kanawa suna shan romon dimukuradiyya –Rahotonmu

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Dimokuradiyya ta haifar da gagarumin ci gaba ta kowane fanni na zantakewar al’umma musamman idan aka rabauta da shugabanni masu kishin al’umma da kuma ci gabansu.

Sannan su kansu al’umomi da ake yi wa shugabanci, su ne suke da alhakin zaben wadanda suke kyautata zaton cewa, za su yi masu jagoranci na adalci da kuma samar da ayyukan alheri kamar dai yadda ake gani a wannan lokaci.

A jihar Kano, gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya yi kokari kwarai da gaske a shekaru kusan 7 da ta yi tana mulkin jihar duk da irin kalubalen tattalin arziki da na siyasa da aka fuskanta a wadansu lokuta wanda hakan ta sanya ake kallon gwamna Ganduje a matsayin shugaba nagari.

Bincike da wata kafar yada labarai da zakulo bukatun al’umma water “ Media Action-Nigeria” ta gudanar ya nunar da cewa, jihar kano ita ce jiha ta farko a kasar nan wadda ta sami ci gaba ta kowane fanni duba da yadda kowane bangare na fadin jihar ya amfana da wadansu ayyuka muhimmai.

Duk da cewa, akwai karancin yayata ayyukan alheri da gwamnatin jihar Kano ke gudanarwa da wadanda ta gudanar, amma dai bincike ya nunar da cewa, gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje tayi fice wajen samar da aiyukan raya kasa kuma duk da kalubalen tattalin arziki da ake fama da shi a wannan karni.

Media Action-Nigeria ta sami kai ziyara kananan hukumomi 44 na jihar Kano inda ta duba irin nasarorin da gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta samu daga shekara ta 2016 zuwa yau, kuma a cewa, kodinetan kafar sadarwar, Malam Jabiru Hassan, za a wallafa cikakken rahoto kan wadannan nasarori domin kara isar da ayyukan alheri na gwamna Ganduje.

A karshe, kafar yada labarai da sadarwa ta Media Action-Nigeria za ta gudanar da jin ra’ayin al’ummar jihar yankunan karkara da birane domin su bayyana irin ribar dimokuradiyya da suka samu a gwamnatin ta Ganduje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *