Kano ta Arewa, Zabinmu Barau Jibrin -Mai Gemu Kwa

Zuwa ga Sanata Barau I. Jibrin

Zuwa ga Sanata Barau I. Jibrin

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

An yi kira ga al’ummar shiyyar Kano ta Arewa da su sake zabar, Sanata Barau Jibrin Maliya a zaben da ake shirin gudanarwa damon ci gaba da samun ribar dimokuradiyya a yanki.

Kiran ya fito ne daga Alhaji Adamu Hedimasta mai Gemu da ke garin Kwa cikin yankin karamar hukumar Dawakin Tofa, inda ya nunar da cewa, ko shakka babu, Sanata Barau Jibrin Maliya wakili ne nagari.

Mai Gemu Kwa ya ce, lokaci ba zai bari a lissafa dukkanin ayyukan alherin da Sanatan ya aiwatar a kananan hukumomi 13 da ke shiyya rba, ko shakka babu al’ummar mazabar sun shaida cewa, wakilcin sa ya haifar da alheri sosai a yankunansu.

Haka kuma ya sanar da cewa, idan aka sake zabar Sanata Barau Jibrin, shiyyar za ta zamo abar misali cikin Nijeriya, duba da yadda da kishin ci gaban dimukuradiyya da kuma al’ummarsa kamar yadda ake gani a kowane lungu da sako na kananan hukumomin da ke karkashin mazabarsa.

A karshe, Alhaji Adamu Hedimasta mai Gemu Kwa ya bayyana cewa, suna nan sun himmatu wajen ci gaba da kokari wajen bayyana alfanun sake zabar Sanata Barau Jibrin Maliya a matsayin Sanatan Kano ta Arewa a dukkanin guraren taruwar al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *