Daga Jabiru Hassan
Babu shakka gwamnatin jihar Kano bisa jagorancin gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje tana samun kyawawan nasarori wajen ganin ana tsabtace muhalli tare da kyautata yanayin guraren zama da kasuwanci a cikin shirin “tsaftar muhalli duk karshen wata”.
Wakilinmu ya hada wani rahoto wanda kuma ya kunshi jin ra’ayoyin al’ummar gari da masu ruwa da tsaki kan harkar kula da muhalli da kuma na fannin kula da lafiya, inda dukkanin wadanda suka sami ganawa da Albishir suka bayyana cewa, ko shakka babu, gwamnatin Ganduje ta ciri tuta ta sha’anin kula da tsabtar muhalli.
Tun da farko sai da kwamishinan ma’aikatar kula da muhalli, Dokta Kabir Getso ya gudanar da zagayen ma’aikatu da hukumomin gwamnati, domin ganin yadda suma suke tafiyar da na su aikin tsabtar muhallinsu a karshen wata, wanda aka fi sani da “Enbironmental Sanitation”, inda ya kan yi bayanai na karfafa gwiwoyin wadannan ma’aikatu da hukumomin gwamnati dangane da kyautata yanayingurarensu na aiki.
A hedikwatar hukumar kula da manyan makarantu, watau “ Kano State Polytechnic”, inda kwamishinan ma’aikatar kula da muhallin ya ziyarta kwanakin baya, ya yaba wa shugaban hukumar, Dokta Kabir Bello Dungurawa dangane da kokarin da yake yi, wajen ganin ana tsabtace gurin da sauran makarantun da ke karkashin kulawar hukumar.
Ya jaddada cewa, gwamnatin Ganduje tana kara daukar matakai na ganin kowane muhalli yana cikan yanayi mai kyau, domin tabbatar da cewa, shirin kula da lafiya yana tafiya sosai ganin cewa, sai da kyakykyawan muhalli ake samun ingantuwar duk wani shiri na kula da lafiya, tare da yaba wa al’ummar jihar Kano, saboda goyon bayan da suke bai wa shirin tsabtar muhalli a fadin jihar.
A nasa bangren, shugaban kwamitin koli na kungiyoyin aikin gayya na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Garba Aminu Kofar Na’isa ya bayyana cewa “ a namu bangaren, muna kokari wajen hada kawunan kungiyoyin aikin gayya da ke fadin jihar Kano, wajen gudanar da aikace-aikace musamman wajen yashe magudadun ruwa da kwatoci da yin ciko inda ruwa ke kwanciya da kuma kwashe shara domin samar da yanayi mai kyau ga muhallinmu”.
Ya ce, sai dai suna da bukatar karin kayan aiki, domin ganin kowace kungiyar ta mallaki na ta kayan aikin, ta yadda za’a rika yin ayyuka cikin sauki da sauri, ya gargadi al’umma da su daina cushe magudadun ruwa ko yin gini kan hanyoyin ruwa ko kuma jibge kasa ko yashi ko kuma dutse kan hanyar ruwa, wanda hakan yana taimaka wa wajen ambaliyar ruwa musamman da damina.
A karshe, wani dan kungiyar taimakon kai da kai daga karamar hukumar Dawakin Tofa, Malam Musa Umar ya yi kira ga kwamitin koli na kungiyoyin aikin gayya na jihar Kano bisa jagorancin Alhaji Ibrahim Garba Aminu Kofar Na’isa, da ya sanya kungiyoyin aikin gayya na yankunan karkara cikin jadawalin samun kayan aiki idan gwamnati ta samar, domin a cewar sa, suna aikin gyaran hanyoyi da yin ciko inda ruwa ke kwanciya da kuma share kasuwanni da makarantu da masallatan Juma’a.