Kano ta dakile sayar da miyagun kwayoyi -In ji Idris Danjalawa

Tura wannan Sakon

Gwamnatin jihar Kano a karkashin gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ta dakile sayar da miyagun kwayoyi masu sa maye a kasuwannin da ake sayar da magani irin na zamani da ke jihar, idan aka yi la’akari da shekarun baya.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin daya daga cikin masu sanar da ke jihar, Al­haji Idris Danjalawa, a lo­kacin da yake zantawa da manema labarai kwanakin baya.

Idris Danjalawa ya koka a kan sabuwar kasu­war da aka tanada domin ‘yan maganin da ke Dan­goro a kan hanyar zuwa Zariya cewa, shagunan sun yi tsada matuka ta yadda ‘yan kasuwar da ke sana’ar ba za su iya mallaka ba, musammanm masu kara­min karfi, kashi 50 daga cikin masu sana’ar kashi 30 marasa karfi ne babu yadda za su iya kama shaguna a sabuwar kasuwar.

Malam Idris A. Salihu, ya ce, yawancin masu nuna sha’awar a koma sabu­war kasuwar masu karfi ne sosai, amma ba kanana ba kamata ya yi a ce duk mai sha’awar komawa ya koma wanda kuma ba shi da sha’awa ya samu wani wuri na daban.

Daga karshe, ya sha­warci gwamnati da ta dubi lamarin da kyau domin yin abin da ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top