Kano ta gabatar da kudurorin gwaji kafin kulla aure

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kudurin dokar tilasta yin gwaji kafin a yi aure a jihar.
Dan majalisar jihar ta Kano mai wakiltar Takai Dokta Musa Ali Kachako, shi ne ya gabatar da wannan kuduri a zauren majalisar wanda aka tafka muhawara a kai kafin a kai ga amincewa da shi.
Ya kuma shaida wa Albishir cewa, lallai ne jama’a sun yi maraba da wannan kudiri a bisa yadda suka rika sa mun martani da rahotanni daga jama’ar jihar.
‘’Wannan kuduri na yi masa kallo na tsanaki kafin in fitar da shi, kuma mun gudanar da dogon bincike a kansa saboda muhimmancinsa kafin a kai ga amincewa da shi,’’ in ji dan majalisar.
Ya kuma kara da cewa, kudurin da yake so ya tsarkake, kana ya taimaka wa tsarin auratayya saboda irin cututtukan da suke yanzu a duniya.
Ya ce: ‘’Misali uku daga cikin manyan cututtukan da suka addabi duniya ba wai a jihar Kano ko Nijeriya ko kuma Afirka kadai ba, cututtuka ne wadanda kuma suna da hanyar matakan da za a iya kare su.’’
‘’Cututtuka ne masu yaduwa, cututtuka ne da daya ta hanyar jima’i ake samu, yayin da kuma daya ake gadota ta hanyar jini da sauransu,’’ in ji shi.
Kachako ya kuma ce da farko kudurin ya yi kallo a matsayin jihar Kano, da yawanta, da muhimmancin al’ummarta, da kuma addini da al’ada. Domin haka kudurin ya kalli abin da Musulunci ya tanadar, abin da al’ada ta tanadar, da kuma abin da zamantakewa ta tanadar.
Saboda haka ya ce idan an yi wannan doka za ta wajabta cewa, a duk lokacin da za a yi aure sai an dauki matakin na yin gwaje-gwaje sannan a samu takardar shaidar da ta tabbatar da cewa, daga hannun kwararrun likitoci suke na bincike domin a yi auren ba tare da cutarwa ba.
‘’Mataki ne da idan an yi shi zai taimaka wa lafiyar al’umma, zai takaita yaduwar cututtuka a tsakanin al’umma, zai taimaka wa ‘ya’yanmu su tashi cikin koshin lafiya, da yaduwar irin wadannan cututtuka, kamar cutar kanjamau, da cutar hanta da kuma cutar amosanin jini ko sikila,’’ kamar yadda ya ce.
Nan da dan lokaci kankani ne dai ake sa ran ‘yan majalisar za su gabatar da kudurin a gaban gwamnatin jihar Kano domin ya zama doka.
Tuni da ma wadansu jihohin kamar Jigawa mai makwabtaka da jihar Kano da kuma wadansu wuraren a jihar ta Kano suka yi nisa wajen irin wadannan gwaje-gwaje kafin a yi auren.