Kano ta rufe asibitin yara -Saboda rashin gamsuwa

Daga Nasiru Muhammad
Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta rufe ayyukan asibitin yara da ke titin Gidan Zoo a cikin birnin Kano bayan shafe kusan shekaru uku da fara aiki.
Matakin gwamnatin na Kano ya dai kawo tsaiko wajen harkokin duba marasa lafiya, sakamakon yadda ma’aikatan asibitin suka gaza sanin makomarsu yayin da marasa lafiya ke kokawa.
Wakilinmu wanda ya ziyarci asibitin yara na Isyaka Rabi’u da ke hanyar gidan adana namun daji, ya ce a sabanin yadda asibitin ke cika makil da marasa lafiya da koke-koken yara, a yanzu shiru kake ji.
Wasu daga cikin marasa lafiya da ke jiyya da kuma ba a sallame su daga asibitin ba, sun yi tagumi suna tunanin a makomar rayuwa, sakamakon fargabar halin da za su shiga idan likitoci da malaman jinya suka daina zuwa aiki.
“Ba mu san makomar mu ba, saboda babu wani bayani da akai mana, wadanda ke kula da asibiti da shugabannin asibitin ne suka samu sabani, don haka sai an warware matsalar,” in ji shi. Sai dai shugaban hukumar da ke kula da asibitoci a Kano, Dr Nasiru Kabo, ya shaida wa BBC cewar gwamatin Kano ba ta rufe asibitin ba, amma ta janye yarjejeniyar kawance aiki tsakanin ta da kamfanin Northfield Health Services saboda rashin gamsuwa da yadda yake kula da asibitin