Kansila Garba Daho ya yaye dalibai 270 kan sana’o’i

Kansila Garba Daho ya yaye dalibai 270 kan sana’o’i

Kansila Garba Daho

Tura wannan Sakon

Daga Mohammed Ahmed Baba Jos

A ranar Lahadin makon jiya ne, Auwalu Baba Ladan kansila mai wakiltar mazabar Garba Daho da ke cikin garin Jos, ya ja damarar tallafa wa jama’ar mazabarsa, musamman ‘yan mata da matan aure gurin kowa masu sana,I’o daban-daban, kansilan ya yi taron yaye dalibai 270 da ya gudana a dakin taro na jama’atu dake garin Jos.

Taron ya sami halartar manyan ‘yan siyasa da shugabanni, kamar shugaban karamar hukumar Jos ta arewa, Alhaji Shehu Bala Usman, da ‘yar majalisa jihar filato mai wakiltar ta arewa maso yamma, Ester Simi Dusu, da tsohon kakakin majalisar jihar Filato, Peter azi da daukacin kansiloli Jos ta arewa.

A jawabin Mista Ester Simi Dusu ta bayyanna cewa,”ta yi murna sosai kuma jama’arsa ba su yi zaben tumun dare ba, kuma ta ja hankalin wadanda aka koyawa sana’ar cewa, za su iya samun ci gaba a kasuwancinsu ba sai suna da yawan jari ba.

Shi ma shugaban taron kuma shugaban karamar hukumar Jos ta arewa, Shehu Bala Usman, ya yi jawabin godiya ya ce”ba kowa ba ne zai sami aikin gwamnati, sun shirya shirin kuma an fara a mazabar Garba Daho, ya kara da cewa, kowace mazaba an ba su Naira milliyan 2 domin fara shirin.

Shugaban ya sha alwashin tallafa wa harkar ilmi da kawo karshen sara suka da masu kwacen waya a cikin garin Jos, a nasa jawabin wanda ya shirya taron da daukar nauyi koyar da sana’o’i, kansilan mazabar Garba Daho, Auwalu Baba Ladan ya ce,”sun koyawa mutane 270 sana’oi daban-daban domin dogaro da kai.

Ya kara da cewa, sun kashe kudi fiye da Naira milliyan 2 domin bayar da gundunmawar su kansilan an yaba masa sosai yadda ya bayar da irin tallafin wannan shirin domin kawar da zaman banza. Shi ma Sulaiman Yahaya Kwande ya turo wakili da tallafin Naira dubu 50.

Daya daga cikin daliban da suka amfana Nafisa Sani Ibrahim, wacce ta koyi kwalliya ta nuna godiyar ta ga wannan kansilan, akwai dalibai da dama da suka koyi yin cake car wash da turare da dinki d shampoo da girkegirke da sauransu kuma sun ce ba su biya ko sisi ba, kansila shi ya dauki nauyin komai da komai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *