Karamar hukumar Gwale ta pdp ce –Awilo

Tura wannan Sakon


Daga Musa Diso

Dan takarar neman kujerar majalisar jihar Kano a karkashin jamiyar PDP a karmar hukumar Gwale Hon. Abdulhadi Dalhat Awilo ya bayyana cewa kasha 90 daga cikin 100 alummar karamar hukumar Gwale duk yan jamìyar PDP ne wannan ya nuna cewa jamiyar PDP a karamar hukumar zata ci zabe ba tare da wata matsala ba.

Dan takarar yayi wannan jawabi ne ga manema labarai jim kadan bayan bikin yaye dalibai 202 da akayi a makarantar B. Paradise wanda aka gudanar a harabar makarantar dake kan titin Aminu Kano a babban birnin Kano satin da ya gabata, Yace babu ko tantama jamiyar PDP lokaci kawai take jira na ranar zabe da magoya bayan Jamiyar zasu kawo chanji da kowa ke so, da ya shafi juyawa jamiya APC baya a daukacin zababbukan da zaayi, tun daga na majalisar jihar Kano, na wakilai dana tarayya da kuma na shugaban kasa.

Awilo ya kara da cewa baa karamar hukumar Gwale kawai ba, duk wanda yasan yadda jamiyar APC ta samu mulki a tarayya da kuma wasu jahohi har da jihar Kano babu shakka, wannan jamiyar, a cewar sa, ta tsoma alumma cikin matsaloli da ba zasu musaltu ba wanda ya hada da rashin tsaro, rashin aikin yi ga matasa maza da mata, rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma bunkasar tattalin arzikin kasa.

Daga karshe yayi kira ga yan Najeriya dasu fito ranar zabe kwansu da kwarkwatarsu dasu juyawa jamiyar APC baya kuma su zabi jam`iyar PDP daga sama har kasa domin itace mafita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *