Karancin abinci a Nijeriya, rashin tsaro –Tumfafi

Karancin abinci a Nijeriya, rashin tsaro –Tumfafi

Karancin abinci a Nijeriya

Tura wannan Sakon

Kamar yadda aka sani cewa, duk kasar da take fama da rashin tsaro babu shakka tana fuskantar kalubale babba wanda idan ba a dauki mataki ba zai haifar da da mai ido ba, in ji Kwamared Rabiu Abubakar Tumfafi sakataren kungiyar kassuwar hatsi da ke Dawanau.

Ya ce, tabbas tsaro na daya daga cikin ci gaban al’umma kuma wajibi ne gwamnati da shugabanni su kare dukiyar al’umma da rayukansu domin wanzuwar arzikin kasa da ci gaban al’umma. Tumfafi ya yi jawabin a lokacin da yake zantawa da wakilin jaridar Albishir a birnin Kano makon da ya gabata.

Ya ce, karancin abinci da ake samu a Nijeriya ya faru ne saboda hana manoma gudanar da aiyukan noma a kauyukansu saboda rashin tsaro domin haka ya kamata gwamnati ta dauki mataki dominn ganin ta kawo karshen al`amarin.

Sakataren ya ce, burinsa shi ne ya ga cewa, kasuwar Dawanau wadda kasuwa ce ta kasa da kasa kuma kasuwa ce ta kayayyakin amfani gona mafi girma a fadin Afirka ta yamma ta rike kambunta a matsayinta uwa kuma jagora a duniya, domin haka yana kira ga al’umma da su ci gaba bayar da goyon baya domin ganin cewa, an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasuwar.

Tumfafi ya yaba wa shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Ado Tambai Kwa saboda jajircewarsa wajen tallafa wa kasuwar domin ganin an cim ma nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *