Karancin ruwan famfo ya addabi birnin Jos da kewaye

Tura wannan Sakon

Daga Mohammed Ahmed Baba Jos

A cikin ‘yan lokutan nan cikin ga­rin Jos na fama da karancin ru­wan sha abin ma yafi azzara a cikin ‘yan satittikan nan inda ake dau­kar tsahon lokaci ba a kawo ruwan ba.

Duk wanda yasan garin Jos a baya yasan gari ne da ko da yaushe ake sa­mun ruwan famfo ba kakkautawa, amma daga baya al’amarin ya canja amma akasari mazauna cikin gari suna zargin ana bai wa wadanda suke bayan gari inda suke cewa, wahalar ruwan iya cikin gari ne kawai inda hausawa suka fi yawa.

Dama a kan bayar da ruwan ne sau daya ko sau biyu a sati to amma a ‘yan lokutan nan sai akai kimanin sati 2 ko 3 ba’a kawo ba, inda ake siyan jarka Naira 20 amma a yanzu jarka ta kai Naira 30 unguwanni masu nisa ma ya kai Naira 40.

Wani lokaci na siyan ma ya zama aiki to, wannan al’amari yana tayarwa da mutane hankali idan a baya ba a san wannan lamarin ba, unguwar layin Ma­jema da ke Bauchi road cikin gari sun koka sosai inda suke cewa, ko da an kawo ruwan ma jifa-jifa baya wuce awa daya ko biyu an dauke inda da dama basa samun ko bokiti daya.

A nasu bangaren hukumar ruwa sun ce rashin wutar lantarki ne so da yawa yake hana samun ruwan sosai, sannan na biyu sukan koka dangane da rashin biyan kudin ruwan inda suke kokawa da cewa, mutane da yawa ma sun man­ta rabon da su biya kudin ruwa amma jama’a na cewa, ai inda ana bayar da ruwan to ko nawa ne za su biya.

Daga nan ake zargin su kansu hu­kumar rarraba ruwan cewa, sai loka­cin damina suke sako ruwan sosai, saboda gudun kada dam din ruwan da ake kira Laminga dam ya fashe ganin cewa, duk wanda yasan garin Jos gari ne da ake sheka ruwa kamar da bakin kwarya amma ana sa ran gwamnati za ta magance matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *